DAGA LARABA: Adawar Gwamnonin Arewa da Ƙudurin Haraji: Kishin Ƙasa Ko Son Zuciya?

Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da ƙudurin Shugaba Tinubu na ƙarin haraji, ko kuma son zuciya?

DAGA LARABA: Adawar Gwamnonin Arewa da Ƙudurin Haraji: Kishin Ƙasa Ko Son Zuciya?

Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da ƙura.

Ɗaya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke shi ne na ƙin amincewa da wani ƙuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa.

Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da ƙudurin ko kuma son zuciya?

Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta.

Domin sauke cikakken shirin, latsa nan

Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja