DAGA LARABA: Shin da gaske ana iya canza janareta ya koma amfani da gas?
Wannan dai wata sabuwar fasaha ce aka kirkira bayan tsadar fetur

Janareta mai amfani da Gas
Tsadar man fetur a Najeriya ya tilasta wa jama’a masu injinan janareta a gida da wuraren kasuwanci sauya masa fasali ya koma amfani da gas din girki.
Wannan dai wata fasaha ce da wasu mutane suka kirkira bayan sun yi nazari a kai.
- DAGA LARABA: Rayuwar ‘Yan Najeriya A Kasashen Waje
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Ya Sa Shinkafa ‘Yar Gida Ke Ƙara Tsada
A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba alfanu ko akasin hakan da za a iya samu game da wannan sabon salo da aka kirkira.
Domin sauraren shirin ko saukewa kaitsaye, ku latsa nan