DAGA LARABA: Da Gaske ’Yan Arewa Ba Sa Fita Kasashen Waje?
Batun ya dauki sabon salo a shafukan sada zumunta, inda ’yan Kudancin Najeriya suke wallafa bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa ƙasashen waje?

Wata muhawara da ta karaɗe shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita ƙasashen waje.
Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan Kudancin Najeriya suke wallafa bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa ƙasashen waje?
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Shaukin Ranar Samun ’Yancin Kai?
- DAGA LARABA: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan