DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
Bayan wasu jihohi da suka maida gwajin jini kafin ayi aure doka, a yanzu wasu alummomi da dama suma sun rungumi irin wannan gwaji duk da ba doka bane a jihohin su.
zamu ji dalilan da suka sa wadannan alummomin suka rungumi gwajin jini kafin aure.
Wasu al’ummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi tsarin yin gwajin lafiyar ma’aurata kafin a daura musu aure.
A wasu lokutan, akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure. Matsalolin sun hada da yaduwar cututtuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya
- DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi yin gwajin jini kafin aure.
Domin sauke shirin, latsa nan