DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa

Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa.

DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa

Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya.

Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta.

Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta.

Domin sauke shirin, latsa nan