DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

A ganinku ta wace hanya za a inganta tsarin makarantun tsangaya ta yadda almajirai ba za su riƙa yin bara ba?

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Almajirai na karatu a makarantar Allo

An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Nijeriya a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.
A baya dai waɗannan makarantu sukan samar da mahaddata Alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai.

Sai dai a wannan zamani yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata.

Gwamnatoci da dama dai sun yi ƙoƙarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin karatun na tsangaya, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa.

Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar karatun tsangaya.

Domin sauke shirin, latsa nan

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya