DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya
Hanyoyin da hukumomi ya kamata su bi wajen dawo da martabar karatun tsangaya a Najeriya.
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.
A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai
Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata.
Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa.
- NAJERIYA A YAU: Me ya sa mutane suka dawo daga rakiyar Kirifto?
- DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Rikide Ya Zama Mabaraci
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar.
Domin sauke shirin, latsa nan