DAGA LARABA: Me nasarar John Mahama ke nufi ga ƙasar Ghana?

Shirin Daga Laraba zai yi nazari ne kan nasarar John Mahama a zaben Ghana da kuma kalubalen da zai iya fuskanta a shekara daya na farkon wa’adinsa.

DAGA LARABA: Me nasarar John Mahama ke nufi ga ƙasar Ghana?

A ƙarshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana a zaben al’ummar ƙasar suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata.

Duk da sauran ’yan takara da ya kara da su, ciki har da mataimakin shugaban kasar mai ci, wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar.

Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan nasarar John Mahama a zaben da kuma kalubalen da zai iya fuskanta a shekara daya na farkon wa’adinsa.

Domin sauke shirin, latsa nan

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro

Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya 

Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn