DAGA LARABA: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
Abubuwan da ke kawo hakan da kuma tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma

Yanayin tattalin arziƙi da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a ƙarshen wata, neman wata hanya ta daban da ke kawo ƙarin kuɗaɗe.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.