DAGA LARABA: Me ya sa ‘yan siyasa ke kin yarda da shan kaye a zabe?
Me ya sa ‘yan siyasa ke irin wannan dabi’a duk lokacin da suka yi rashin nasara?
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
A tsarin zabe, dole a samu wanda ya yi nasara, a kuma samu wanda ya fadi. Amma wannan ka’ida har yanzu ba ta samu wurin zama ba a fagen siyasar Najeriya, don kuwa da yawa daga cikin wadanda suka fadi ba sa yarda su rungumi kaddara, sai kaji suna kiran “Magudi aka yi, amma ni na ci zabe”.
Mene ne dalilin da ‘yan siyasar Najeriya ke kin karbar kaddarar faduwa?
- DAGA LARABA: Matakan Samun Nasara A Watan Ramadan
- NAJERIYA A YAU: Matsin tattalin arziki na neman hana yin burodi – Kungiya
Saurari shirin Daga Laraba domin jin dalilin ‘yan siyasa na kirkirar wannan dabi’a ta kin karbar kaye a matsayin kaddara da ke shafa wa Najeriya bakin fenti a idanun duniya.