DAGA LARABA: Ruwan ‘Fiyowata’ Na Neman Ya Gagari Talaka
Wasu masu sarrafa ruwan ledar sun fara rufe kamfanoninsu
Ruwan leda ya zama abin tattaunawa a tsakanin ’yan Najeriya saboda yadda ya yi tsadar da bai taba yi ba.
Wasu na ganin shi ne ruwan sha da ake samu mai dama-dama wajen tsafta, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan ruwa mara tsafta a wasu wuraren.
- Alaƙar Da Ta Rage Tsakanin ECOWAS Da Kuma Nijar, Mali Da Burkina Faso
- Harshen Uwa: Dalilin Da Mutane Ke Mance Yarensu Na Asali
Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu na rufe kamfanoninsu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dalilan da suka jawo hakan.
Domin sauke shirin, latsa nan