DAGA LARABA: Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya?
Tun bayan dawowar dimokradiyya a jamhuriya ta hudu ne ‘yan Najeriya ke ta fatan samun rayuwa mai sauki. Shin ‘yan Najeriya sun cinma wannan fata?
A farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999, dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya ya haifar da babban fata a zukatan ‘yan ƙasa, inda mutane suka yi tsammanin ƙarshen mulkin soja zai kawo adalci, ci gaban tattalin arziƙi, tsaro, da shugabanci nagari da ke sauraron muradin jama’a.
Jama’a sun yi imanin cewa za su sami ‘yancin faɗar albarkacin baki, ingantaccen zaɓe, aikin yi, da rage talauci ta hanyar shugabannin da suka fito daga zaɓin jama’a.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Siyasar Matasa A Najeriya Tun Bayan Dawowar Jamhuriya Ta Hudu
- DAGA LARABA:Yadda Tattalin Arziki Da Ababen More Rayuwa Suke A Farkon Jamhuriya Ta Hudu Da Kuma Yanzu
A cigaba da kawo muku shirye-shirye gabanin muhawarar Daily Trust shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi waiwaye ne don jin irin fatan da ‘yan Najeriya ke da su bayan dawowar Demokradiyya.
Domin sauke shirin, latsa nan