DAGA LARABA: Shin kare kai daga harin ’yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro?
Yayin da alumma da dama a Arewacin Najeriya ke fuskantar harin ‘yan ta’adda, wasu da dama na kira da a tashi don kare kai. Shin ko kare kai daga harin ‘yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro?
Hare haren ’yan ta’adda na ƙara ta’azzara a yankuna daban-daban a faɗin ƙasar nan wanda hakan ke nuni da ƙarin rashin tsaro da ya daɗe yana ci wa al’umma da ma gwamnati tuwo a ƙwarya.
Ko a kwana-kwanan nan an ga yadda Jihar Filato ta yi ta fama da irin waɗannan hare-hare da kuma hare-haren ramuwar gayya.
Wani ƙididdiga da ƙungiyar dake tattara bayanan hare-haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya.
Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan Jihar Binuwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce da ya kai har wasu na kiran mutane su tashi don kare kansu.
Irin wannan kira dai an daɗe ana yi, sai dai gwamnati na ganin ba daidai ne mutane su kare kansu daga hare-haren ’yan ta’adda ba.
- NAJERIYA A YAU: Yawan Kuɗaɗen Da Ake Bukata Don Samar Da ’Yan Sandan Jihohi
- DAGA LARABA: Yadda Talauci Ke Hana Wasu Mata Sayen Audugar Al’ada
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan shin ko kare kai daga hare haren ’yan ta’adda zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya?
Domin sauke shirin, latsa nan