DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
Wata baiwar Allah da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana mana yadda aka yi garkuwa da ita da kuma yadda ta samu ta Kubuta daga hannun masu garkuwa da ita bayan ta sha bakar wahala.
A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.
Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi.
Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa idan an yi garkuwa da ‘yan uwansu?
- NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
- DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
Wannan shine batun da shirin Najriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a akai.
Domin sauke shirin, latsa nan