DAGA LARABA: Tarihin Almajirci a kasar Hausa da yadda yake a da

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi duba ne kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya.

DAGA LARABA: Tarihin Almajirci a kasar Hausa da yadda yake a da

Almajirai na karatu a makarantar Allo

Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren Larabci wato Almuhajir, da ke nufin wanda ya bar garinsa don zuwa wani gari neman ilimi.

Mafi yawan al’ummar Arewa inda aka fi amfani da kalmar almajiri, sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da Musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa.

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi duba ne a kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya.

Domin sauke shirin, latsa nan