DAGA LARABA: Yadda Bude Kan Iyakokin Najeriya Da Jamhuriyar Benin Da Niger Zai Amfani Alummar Kasashen
Yadda Najeriya da Benin da Nijar zasu amfani juna sakamakon bude kan iyakokin kasashen da Najeriya ta yi.
A watan Agustan shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta da wasu ƙasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Wannan mataki a wancan lokaci an ɗauke shi ne domin yaƙi da fasa-kwauri, hana shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma kare tattalin arziƙin cikin gida.
Bayan wannan tsawon lokaci da aka dauka na takaita zirga-zirga tsakanin wadannan kasashe, lamarin ya shafi kasuwanci, da mu’amalar jama’a da kuma rayuwar al’ummomin da ke zaune a kan iyaka.
Sai dai bayan wannan tsawon lokaci a kwanan nan gwamnatin Najeriya ta sanar da sake bude iyakokinta da wadannan kasashe biyu, a wani mataki na farfaɗo da kasuwanci, da ƙarfafa haɗin kai da kuma bunƙasa tattalin arziƙin yankin.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
- DAGA LARABA: Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya?
Ko yaya bude wadannan iyakoki zai amfani kasashen biyu?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan