DAGA LARABA: Yadda Mutane Ke zubar Da Ladar Azuminsu Kafin Sallah
Labarin masu shirya bikin tarbar shaidan a karshen watan Ramadan
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
Malamai na karfafa wa mabiya addinin Islama guiwa a watan Azumin Ramadana wurin tsayuwar daka wurin ibada, amma wani abin mamaki shi ne yadda a karshen watan azumin mutane ke shagalta har su kai ga haramun wurin bikin Sallah.
Shin kuna da labarin masu tara kudi domin shirya bikin tarbar shaidan?
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Zai Faru Idan Aka cire Tallafin Man Fetur
- DAGA LARABA: Yadda rashin ruwan sha ke lakume rayuka a Kano
Shirin Daga Laraba na wannan karon ya dubi hanyoyin da maza da mata ke bi wurin zubar da ladar ayyukan da suka yi a cikin watan Azumin Ramadana.