DAGA LARABA: Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya
Ta wadanne hanyoyi ne rage farashin man fetur a Najeriya zai yi tasiri ga rayuwar ‘yan Najeriya?
Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa kasuwanni.
Saboda haka, duk wani sauyi a farashin mai kan yi tasiri kai tsaye ko a kaikaice ga farashin kayan masarufi da ’yan Najeriya ke amfani da su a kullum, kamar abinci, da kayan gini, da magunguna da sauransu.
Sai dai tambayar da ke yawan fitowa ita ce: shin rage farashin mai zai kai ga rage farashin wadannan kayayyaki?
- NAJERIYA A YAU: Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas
- DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan