DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya
Shirin Daga Laraba na wannan makon yayi nazari ne kan yadda sinadaran dandanon abinci ke haifar da illa ga lafiyar mutum.
A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu.
Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsaloli ga lafiya.
Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, suna iya haifar da illa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma
- DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan irin matsalolin da amfani da sinadarin dafa abinci fiye da kima ke jawowa ga lafiyar mutane.
Domin sauke shirin, latsa nan