Daga littafin Magana Jari Ce muka tsamo fim din gargajiyar Bahaushe – Bashir Rijau
Bashir Rijau ya kasance mai shiryawa da ba da umurni a fina-finan Hausa. A kwanakin baya ya fitar da wani kayataccen fim dinsa mai suna Sarki Jatau. Ya tsamo labarin fim din ne daga shahararren littafin nan na Magana Jari Ce na marigayi Dokta Abubakar Imam. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda fim din […]
Bashir Rijau ya kasance mai shiryawa da ba da umurni a fina-finan Hausa. A kwanakin baya ya fitar da wani kayataccen fim dinsa mai suna Sarki Jatau. Ya tsamo labarin fim din ne daga shahararren littafin nan na Magana Jari Ce na marigayi Dokta Abubakar Imam. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda fim din ya dauki hankalin al’umma, musamman yadda fim din ya fitar da al’adun gargajiyar Malam Bahaushe. Ga yadda ganawar ta kasance:
Ko za ka yi mana takaitaccen bayani game da kai kanka, musamman yadda ka shafi al’amuran fim?
Kamar yadda sunana ya nuna, an haife ni ne a Rijau, wato garinmu ke nan da ke Jihar Neja. Na yi makaranta a Kontagora, na yi makarantar sakandare a Kagara. Daga nan na samu gurbin karo ilimi a Jami’ar Ahmadu Bello zariya. Na yi kwas a kan aikin dab’i, inda bayan na kammala sai na samu aiki a Abuja, kamfanin buga mujallu da sauran ayyukan dab’i, mai suna Heritage Press. Na samu kusan shekara goma sha biyu ina aiki a nan. Bayan na aje aiki da su sai na bude kamfanina mai suna Grafarts Consult Ltd. A nan ne na rika gudanar da ayyukan dab’i da shirya fina-finan Hausa.
Ya zuwa yanzu, fina-finai nawa ka shirya?
Ba wai na maida hankali ga fim kacokan ba ne, domin sha’awa ce ta sanya na shiga harkar fim, don haka idan na samu dama nakan saka jari in shirya fim. Ya zuwa yanzu dai na shirya fina-finai kamar guda shida.
A kwanakin baya, ka shiga harkar wallafa mujalla mai suna Abida, wacce ta ke ba da labarin al’amuran fina-finai da sauransu, shin me ake ciki ne game da mujallar?
Babu shakka, ni da sauran abokaina, mun taru mun hada jari da karfi wuri guda muka shirya mujallar Abida. Kodayake ta sauya zubi da tsaftar aikin dab’in mujallun Hausa a wancan lokacin amma kamar yadda ka sani shirin mujalla akwai matsaloli da dama, wadanda sukan bijiro. Cikin yardar Ubangiji, ba mu yi tafiya mai nisa ba a cikin shirin mujallar, saboda matsalolin nan sai muka saka ta a ragaya amma muna sa ran nan ba da dadewa ba, ita ma za mu dauko ta mu kakkabe ta, mu sake shigar da ita kasuwa.
Sai ga shi a ’yan kwanakin nan ka fitar da wani fim mai taken Sarki Jatau, shin ya wannan fim yake?
Fim din Sarki Jatau, mun samo labarinsa ne daga cikin mashahurin littafin nan na Magana Jari Ce, na Malam Abubakar Imam, wanda hazikin marubuci ne. Da muka duba labarin sai muka ga ya kusan zuwa daidai da irin abin da muke son mu nuna a fim din, musamman abin da ya shafi bangaren al’adu na Hausa, ganin irin yadda labarin yake da tsafta. Saboda haka sai muka je kamfanin NNPC da ke ginin Gaskiya Corporation Zariya, muka nemi izinin yin amfani da shi a fim. Sun ba mu damar yin haka a rubuce, daga nan muka shiga gadan-gadan wajen shirya fim din. Duk dai ma’abucin karatun Magana Jari Ce, ya san labarin Sarki Jatau, don haka mun mayar da shi fim.
Wane dalili ya sa kuka dauki tsohon labari kuka juya shi zuwa fim duk da cewa zamani ya canja?
Dalilin da ya sanya muka dauko wannan tsohon labari shi ne, domin mu bunkasa al’adun gargajiyar Malam Bahaushe. Mun yarda da cewa Bahaushe na da labarai sahihai kuma ko cikin marubutanmu da suka gabata, Allah Ya hore masu basira na labarai wadanda za a iya amfani da su ko a wannan zamani mutane su karu. Saboda haka gargajiyancin yana daya daga cikin dalilan da suka sa muka dauki labarin Magana Jari Ce. Kuma kamar yadda kuka gani a fim din, kusan duk abin da za ku gani a gargajiyance muka sanya shi, in ban da ’yan wasu abubuwa da ba a rasa ba. Ina jin dalili ke nan ya sanya ma fim din ya samu daukaka saboda a gasar karramawa ta Kannywood da ta gabata kwanakin baya, mun samu shiga matakin farko, cikin gurabe kusan guda bakwai. daya daga ciki akwai abin da ya shafi suturar gargajiya da muka yi amfani da ita a fim din da kuma nuna al’adu na Bahaushe. Haka kuma wata gasar irinta da aka yi a Kaduna kwanakin baya mu ne fim din da muka zama zakara wajen nuna al’adun Malam Bahaushe. Alhamdu lillahi, mun yi iyaka kokarinmu. Kuma ka san mutum tara yake bai kai goma ba, ba a rasa ’yan kura-kurai na da can ba.
Ganin cewa shirin ya amsu a nan gida, wane buri gare ka wajen shigar da shi sassan duniya?
A halin yanzu ma fim din na daya daga cikin wadanda aka zaba, wadanda za su shiga gasar Caine Award ta duniya, wacce za a yi a kasar Faransa. Mun riga mun dora shi kuma an yi masa rijista, kuma cikin hukuncin Ubangiji za a tafi da shi nan da makonni biyu masu zuwa in Allah Ya yarda. Ka ga a can tun da babbar kasuwa ce ta baje kolin fina-finai na duniya baki daya, watakila wasu za su ga aikin da muka yi, a zabe shi kuma mu samu karamomi da ba mu ma yi zato ba.
Wasu matsaloli da bincike ya nuna kuke fuskanta, su ne na satar fasaha da sauran dangoginsu, wane shiri kake yi don kare wannan fim naka daga fadawa cikinsu?
Wannan gaskiya ne, domin satar fasaha babbar matsala ce da muke fuskanta wacce ke ci mana tuwo a kwarya a masana’antar shirya fina-finan Hausa. A yanzu abin ma har ya wuce tunaninka, domin a can watakila fim dinka za a kwafa, a buga shi a sayar a kudi kalinan, to amma yanzu abin ya kai sai a kwarfe fim din naka, a zura shi cikin kwamfuta, a rika tura wa mutane cikin waya kan Naira hamsin-hamsin. Ka ga wannan babbar matsala ce. Wannan aiki ne da muke ganin kamar ya shafi hukuma, domin ita ke da karfin da za ta iya shigowa ta taimaka mana. Saboda duk wani hakki da ake biya ga hukuma muna biyansa. Muna biyan haraji, muna biyan kudin hakkin mallaka da sauransu. To saboda haka duk wanda ya karya dokar kasa ko ya cuci wani, kamata ya yi hukuma ta fito ta hukunta shi kuma ta hana wannan laifi ya ci gaba da gudana. Don haka muna rokon hukuma ta fito ta taimaka mana a wannan yaki da satar fasaha.