Daga masu karatu: Martani a labaran auratayya

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili. Ga ci gaba daga sakonni masu dauke da kyawawan misalai ga ma’aurata; da fatan za ku ci gaba da aiko da naku sakonnin ta shafukan sadarwar watsaf ko fesbuk a rubuce ko murya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu baki daya, amin. Na karanta […]

Daga masu karatu: Martani a labaran auratayya
Daga masu karatu: Martani a labaran auratayya

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili. Ga ci gaba daga sakonni masu dauke da kyawawan misalai ga ma’aurata; da fatan za ku ci gaba da aiko da naku sakonnin ta shafukan sadarwar watsaf ko fesbuk a rubuce ko murya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu baki daya, amin.

Na karanta labarin Hajiya Baraka, gaskiya mijinta ya ci amanar zaman tare; ni ma haka na sha wahala da mijina yau akwai, gobe babu  har Allah Ya azurta shi. Ya kammala digiri  kuma ya dace da samun aiki mai tsoka; da ya tashi karin aure bai gaya min ba sai da abu ya yi nisa ’yar uwata ta ji ta gaya min. Hankalina ya yi matukar tashi, ba tsoron kishiya ne ya tayar min da hankali ba, irin yadda yake yin abin a boye ba tare da ya sanar da ni ba; wannan ya sa nake tunanin ko ya yi auren ma haka zai rika yi min. Na ga fadi-tashin da muka sha tare ya kamata a ce ni na fara sanin wannan abu kafin wani; na tunkare shi da batun ina kuka; abin mamaki shi ma fashewa da kuka ya yi ya ce min “Wallahi Saude na kasa yadda zan tunkare ki da batun nan saboda kin min halacci kuma duk inda mace tagari ta kai kin kai, bai kamata a ce na yi miki kishiya ba, amma kin san kaddara ta riga fata. Wallahi ba niyya ta in wulakanta ki ba saboda karin aure; kuma ba hakan na nufin matsayinki da kaunarki sun ragu a zuciyata ba, iyaka dai bukata ce da Allah Ya kaddaro min. Kuma in har na yi amfani da wannan damar na wulakanta ki to ina rokon Allah Ya saka miki cikin gaggawa. Don Allah ki yi hakuri, ki yafe min Saudena!” Shi ke nan na kwantar da hankali. Nan na shiga ni ce gaba a komai na shagalin bikin; bai min lefe ko wasu manyan kyautar dannar kirji ba; amma kyakykyawar dangantakar da ya rika nuna min ya fi min kowane irin kayan duniya. Babbar kyautar da ya ba ni ranar da aka kawo amarya; ya dauke ni yawon cin abinci a wani tsadajjen wajen cin abinci, a teburin da ya sa aka tsara musamman don ya nuna yanayin romansiyya, furanni ga kyandir-kyandir an kuna; sannan ya saka mini wani hadaddden zoben lu’u-lu’u (diamond) a yatsata. Daga nan kuma ya kai ni super market ya saya mini turaruka da kayan shafa masu tsananin tsada da haduwa; ba mu muka koma gida ba sai wajen karfe 2 na dare; kuma ya kasance tare da ni a wannan daren tare da nuna min tsananin kulawa wacce har gobe take sa ni farin ciki. Kuma da giyar amarci ya dibi amarya ta fara raina mini wayo, tun tana yi mu kadai har ta yi a gabansa, ya ja mata kunne ta ki bari, take yanke ya sake ta; haka na shiga na fita har sai da ya mai da ita don dai na san yana son matarsa tun da har ya zabo ta ya auro ta. Ita kuma tunda ta dawo ta gane kurenta ta shiga saiti yanzu muna zaune lafiya. Na kawo wannan labari ne don in nuna ba duka maza ne suke da halin juya wa matansu na farko baya ba, yayin da suka tashi yin sabon aure, kuma ya zama darasi ga sauran maza da suka yi kuskure yadda za su gyara da kuma na gaba yadda ya kamata su yi. Da fatan Allah Ya hada kan dukkan ma’aurata, Ya ba su zaman lafiya, amin.

-Zaujatu Hamza

 

Nabila ina mamakin da ba ki gyara wa wannan da ya ce wai salihar mace na juyewa ta yi abin da wadda ba salihar ba ma ba za ta yi ba; sannan ya ba da misali da wadansu masu sa nikabi da hijabi da asirinsu ya tonu ashe masu bin bokaye ne; ai shi salihanci a zuci da dabi’a ake samunsa ba a tufafi da yawan zuwa Islamiyya ko masallaci ba. Don haka yin kwakwkwaran bincike a kan ainihin halayya da dabi’ar wanda za a aura ta nan ne za a iya gane hakikanin nagarta ko rashinta. Don mace na sa hijabi da zuwa Islamiyya ba shi ke nuna ita saliha ce ba; haka don mace na yafa gyale da sa matsatstsun kaya ba shi ke nuna ita fasika ce ba; halayyarsu da dabai’arsu musamman a cikin yanayi mai tsanani shi ne zai nuna haka. Amma kuma duk wanda yake da nagarta a dabi’a da zuciya, amma kuma yana shiga da ta saba wa addini, ko bai zuwa masallaci da Islamiyya, to nagartasa na da nakasu; amma wadda ke sa hijabi da nikabi ga zuwa Islamiyya a-kai-a-kai, sannan a boye tana bin bokaye; to ni a fahimtata wannan ba ta da wani salihanci ko kadan; wadda ko take da nagarta a dabi’a da halayya, sannan ga hijabi da nakabi da zuwa Islamiyya to wannan ita ce cikakkiyar saliha. Da fatan Allah Ya kara mana yawansu a zuriyya da al’umma, amin.

-Baban Zainab daga Kano.