Daga Musa Kutama, Kalaba Aminiya: Ganin Shugaban Qasa ya fito daga wannan yanki na Neja-Delta ana ganin mutanensa za su goyi bayan a raba qasa, ina ra’ayinsu ya karkata? Dauda Birma: Da muka zo nan Kalaba waxanda suka zo suka ce su ne wakilan Majalisar
Kwamitin Bada Shawara kan Taron kasa ya ziyarci shiyyar Kudu maso Kudu kuma Kalaba ta Jihar Kuros Riba na daya daga cikin jihohin yankin biyu da ya ziyarta. Mutane sun dauka mutanen yankin za su bukaci a raba kasar nan cikin shawarwarinsu amma sai ga shi sun ba marada kunya inda suka ce in kwamitin […]
Kwamitin Bada Shawara kan Taron kasa ya ziyarci shiyyar Kudu maso Kudu kuma Kalaba ta Jihar Kuros Riba na daya daga cikin jihohin yankin biyu da ya ziyarta. Mutane sun dauka mutanen yankin za su bukaci a raba kasar nan cikin shawarwarinsu amma sai ga shi sun ba marada kunya inda suka ce in kwamitin ya je da niyyar zama ne domin a raba kasa to, ya tattara komatsensa ya san inda dare ya yi masa. Wakilinmu ya tattauna da Alhaji Dauda Birma, memba a kwamitin kan lamarin:
Aminiya: Ganin Shugaban kasa ya fito daga wannan yanki na Neja-Delta ana ganin mutanensa za su goyi bayan a raba kasa, ina ra’ayinsu ya karkata?
Dauda Birma: Da muka zo nan Kalaba wadanda suka zo suka ce su ne wakilan Majalisar Mutanen Kudu maso Kudu sun ce idan za a yi taron da za a raba kasa ce, su fa kada a kira su. A wasu wurare da muka tafi mun je Ondo kasar Yarabawa, a can babu mutum daya da ya fito ya ce yana son a raba Najeriya, a can ma kowa na cewa sabon siminti za a kwaba domin a simince zamantakewar Najeriya. Duk inda ake da ’yar baraka a samu a dinke shi domin zaman Najeriya tare ya dada ingantuwa ba a rusa kasar nan ba .
To akwai abubuwa da jama’a ke fadi da yawa maganar tsaro, maganar ilimi, maganar cin hanci da rashawa abubuwa da yawa mutane suna kawowa amma ka san ba mu soma hada su ba, tukuna wannnan dai kowa ya zo zai fadi abin da ya ga dama, mun ba kowa ’yancin ya rubuto takarda ya kawo mana wanda ya zo ya fada mana da baki sai mu ce masa to, ka san fadinka da baki ba ya da fa’ida ba mu shi a rubuce, harkar gwamnati idan ba a rubuce ka bayar ba ba ta amfani, to, mutane suna rubutawa suna kawo mana .
Idan muka gama sai mu zauna mu ga me aka fahimta sannan sai mu rubuta mu aike wa Shugaban kasa. Kuma akwai abu daya da ya kamata in bayyana mutane suna cewa Shugaban kasa ya wuce makadi da rawa ya yi riga Malam Masallaci ya nada kwamiti akwai majalisa akwai me. Shugaban kasa ya fi kowa sanin akwai majalisa ya fi kowa sanin ba ya da iko ya ce a fito ga abin da za a yi sai bayan an hada gaba daya zai kai wa majalisa domin majalisa ita ke da hakkin yin dokoki a kasar nan kuma ya kamata jama’a su sani kafin ma ya kaddamar da wannan kwamiti sai da ya zauna da shugaban Majalisar Dattijai Dabid Mark da na wakilai Waziri Tambuwal suka yarda cewa ya je ya yi wannan abu idan ya tattaro ya kawo musu su kuma za su yi magana da ’yan majalisa domin su samu yarda.
Aminiya: Kuna da yakinin cewa abin da kwamitin ya tattaro ya mika masa ya kai majalisa za ta tattauna batun?
Dauda Birma: Idan muka kai wa Shugaban kasa mun gama namu, abin da za mu yi shi ne mu ba shi a zamanmu na masu hankali, idan zai kai gaba abin zai samu karbuwa. Wato an dade ana kurari ana magana a kan za a yi kaza-kaza, maganar a zauna a yi wannan taro ya kai shekara 30, muna gudun wannan abu yanzu sai ka lura cewa mu da ke Arewa mun yarda a yi wannan taro me ya sa muka yarda? Kullum idan ana ce maka gafara sa, gafara sa, so ake ka gudu, to, amma yanzu mun ce ba za mu gudu ba kowa ya ce zai zo ya yi magana. Yaya za ka ji tsoron maganar da za a yi da baki ba dambe, ba harbi da baki kowa ya kawo tasa hujja, mai hankali ya fada, mara hankali in ya fada a yi masa dariya iya maganar ke nan.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kuka fuskanta daga lokacin da kuka fara zagayen nan?
Dauda Birma: Kusan ba inda muka samu kalubale, duk inda muka ziyarta ko muka je an karbe mu, duk inda muka je an kawo takardu. A Ondo, mutum 38 suka kawo hujjojinsu a rubuce, a Filato mutum 25, a Neja mutum 36.Yanzu a nan na tabbata za mu samu kamar 40. Saboda haka babu wani kalubale babu kuma wani wanda ya ce me ya kawo mu ba wanda ya ce bai yi maraba da mu ba, sai wasu abubuwa da suke fitowa su ba ka mamaki ka ce ashe da ma an san ga abin da mutane suke fadi, da tunda aka yi taron.