Daga taskar tsohon mai hoto BABA SHETTIMA 3

Daga taskar tsohon mai hoto BABA SHETTIMA 3

Laftanar-Kanar Yakubu Gowon, Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Sojan Kasar nan da ya yi mulki a tsakanin 1 ga watan Agustan 1966 zuwa 29 ga Mayun 1976. Ya zama shugaban kasa ne a lokacin yana da shekara 34 bayan wasu sojoji da suka fito daga yankin Arewa sun yi wa Janar Agunyi Ironsi juyin mulki. Ya samu nasara a yakin Biyafara na tsawon shekara biyu da rabi bayan ya fatattaki mayakan da ke karkashin jagorancin Kanar Odumegwu Ojukwu. Birgediya Murtala Ramat Muhammad ne ya yi masa juyin mulki tare da hadin bakin Babban Jami’in Tsaronsa Birgediya Joseph Garba a lokacin da shugaban ya tafi Kampala da ke Uganda don halartar taron Kungiyar Hada Kan Kasashen Afirka (OAU)