Daga taskar tsohon mai hoto BABA SHETTIMA (9

Daga taskar tsohon mai hoto BABA SHETTIMA (9

Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, zababben shugaban qasa da ya yi mulki a tsakanin 1 ga watan Oktoba 1979 zuwa 31 ga watan Disamba, 1983. An sake zabarsa a karo na biyu a shekarar 1983 amma Cif Obafemi Awolowo na Jam’iyyar UPN da Alhaji Waziri Ibrahim na Jam’iyyar UNPP sun kalubalanci sahihancin zaven a kotu amma daga baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Shagari a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben Sai dai a ranar 31 ga watan Disamba 1983 ne Janar Muhammad Buhari ya yi masa juyin mulkin da ba a kashe kowa ba. Gwamnatin Buhari ta tsare shi a wani gida har na tsawon shekara biyu da rabi ba tare da ya ga hasken rana ba al’amarin da ya ja masa matsalar dusashewar ido tun daga wancan lokaci