Daga wakar yabo na zama mawakin kowane fanni – Ado Jume Kafanchan
Ado Jume Kafanchan wani matashin mawaki ne a Kudancin Kaduna wanda ya shahara a fagen wakokin begen da fadakarwa da biki da siyasa da kuma wakokin fina-finai. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce da wakarsa ya taso: Muna so ka fara da gabatar mana da kanka.Sunana Ado Isa Jume. Mahaifina da aka fi sani da […]
Ado Jume Kafanchan wani matashin mawaki ne a Kudancin Kaduna wanda ya shahara a fagen wakokin begen da fadakarwa da biki da siyasa da kuma wakokin fina-finai. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce da wakarsa ya taso:
Muna so ka fara da gabatar mana da kanka.
Sunana Ado Isa Jume. Mahaifina da aka fi sani da Malam Jume shi ne shugaban kungiyar Yabon Manzon Allah ta “Wa Jam’u Rasulullahi’(SAW) na Kudancin Kaduna, kafin Allah Ya yi masa rasuwa gab da watan azumin da ya wuce. Mahaifiyata kuwa Hajiya Asabe, uwa daya uba daya suke da tsohon ma’aikacin BBC, Bala Ibrahim, ita ce gaba da shi. An haife ni a cikin garin Kafanchan kuma nan na yi makaranta tun daga firamare har zuwa kwaleji inda na yi diploma a fannin Harkokin Gudanarwa (Public Administration). Kuma na yi karatun addini na allo a wajen Malam Aminu Kasim, na yi Islamiyya a makarantar Ihya’is Sunnah sannan na dan taba na zaure duk a garin Kafanchan.
Yaushe ka fara waka?
Gaskiya ina iya cewa a cikin waka na taso, kamar yadda na fada maka mahaifina mawakin Manzon Allah ne, shi ne shugaban masu Madahu na Kudancin Kaduna. Tun muna yara yakan ce ku zo mu je mu yabi Manzon Allah (SAW), to daga nan dai abin ya fara.
Ke nan gadonta ka yi?
kwarai kuwa haka ne. Ba ma ni kadai ba, a yanzu haka wanmu Shafi’i Jume shi ne Halifan mahaifinmu kuma kanena Ibrahim Baban Asabe, ana yi masa lakabi da dan Autan masu bege na garin Kafanchan.
Yanzu wakokin da kake yi sun tsaya ga yabo ne ko kana taba sauran fannonin?
Wakokin yabo da su na fara, amma zuwa yanzu babu irin wakar da ba na yi. Wakokin da suka hada da na fadakarwa da ilimantarwa da siyasa da na biki da wakokin fina-finan Hausa, babu wanda ba na yi.
Za ka iya tuna wakar da ka fara rubutawa?
Wakar Yabon Annabi ce mai suna “Ya Allah, Ya Allah dadon fahimta a Yabon Manzo.”
Ya zuwa yanzu ka rubuta wakoki nawa?
Na rubuta wakoki sun kai dubu daya. Daga kasidun yabo zuwa na aure da na fadakarwa da na fina-finai. A rana daya idan na zauna nakan rubuta wakoki hudu zuwa biyar, mafi karanci shi ne in rubuta wakoki uku.
Ko faifan wakoki nawa ka fitar?
Akwai akalla guda goma a kasa wadanda na ba da su talla kuma kowane akalla yana dauke da wakoki 12, akwai irin su ‘Nadiya da ‘Gimbiya Rashida’ da ‘Mai Sona’ da ‘Da Zuciya daya’ da ‘Launin kauna’ da sauransu, sai kuma na kallo guda daya mai suna ‘Rayuwar Zamani.’
Wane alheri ka taba maka da ba za ka taba mantawa da shi ba?
To, gaskiya dai bayan na fitar da wakar Ishiriniya a fiyano mai suna ‘Wa
Jam’u Rasulullahi,’ akwai wani dan siyasa a yankin Ganjuwa ta Yamma a karamar Hukumar da ke Jihar Bauchi, wanda ya taba tsayawa takarar dan Majalisar Dokokin Jihar a karkashin Jam’iyyar CPC, mai suna Bashir Bello da ya ji wakar sai ya kira ni a waya muka gaisa bayan kwana biyu ya biyo ni da kyautar Naira dubu 20 a lokacin, daga baya na yi masa wakokin siyasa ya dauki Naira dubu 100 ya ba ni ka ga shi kam ba zan taba mantawa da shi ba
Ka ce kana taba wakokin fina-finai a wadanne fina-finai wakokinka suka fito?
Farko na fara ne da wakar ‘Launin kauna’ na kamfanin ‘Alkausar Film Production’ da ke Kafanchan sai dai fim din bai fito ba har yanzu. Daga baya na yi wa wata mai suna Hauwa Farar Cika a Kaduna shi ma bai fito ba. Bayan nan a yanzu haka akwai wakokina a wasu fina-finai
da ake sauraron fitowarsu masu suna ‘Musaddik’ da ‘Lokaci Ya yi.’ Guda daya kawai ta taba fitowa a cikin wani fim mai suna ‘Kimiyya da Fasaha,’ na Mustafa Shehu.
Akwai barazanar da ka taba fuskanta a sana’ar waka?
Gaskiya babu, in dai ban da cin dunduniya daga wadanda kuke harkar tare, wadanda idan wani furodusa ya so ba ka aiki in ya biyo ta hannunsu sai su musanya ka da wanda suke so.
Yaya batun kasuwancin kasa-kasan wakokinka?
Matsalar ita ce su ’yan kasuwa suna la’akari da shaharar mawaki ne, duk irin dadin wakarka da kyanta da irin sakon da ke ciki in ka kai musu ita maimakon su yi kokari su tallata ka, sai su kalli daga inda ka fito, ko tunda kai ba ka yi fice ba sai su ijiye. Amma da zarar wanda yayi fice ya kawo nasa duk irin rashin kyanta sai ka ga nan da nan sun karba sun tallata ta. To gaskiya wannan babbar matsala ce da ya kamata ’yan kasuwa su gyara domin in kai ne yau, to ba kai ne gobe ba, maimakon sai wanda na sani, a rika tallafa wa masu tasowa.
Bayan rubuta wakoki akwai wata sana’a ne da kake yi?
kwarai kuwa, ina kasuwancin citta, mukan sayo mu gyara mu sayar wa kamfani. Duk wanda ya taso a Layin Zariya ba za ka rasa shi da harkar citta ba. Bayan kasuwancin citta a yanzu haka ina da dakin rera wakoki na kaina wato Situdiyo a cikin garin Kafanchan wanda ake zuwa buga wakoki daga wurare daban-daban kuma ina da shagon sayar da fina-finai da wakoki mai suna bideo Club.
Wadanne nasarori ka samu a harkar wakoki?
Gasikya alhamdulillahi domin nasara ta farko da mawaki yake nema ita ce a san shi tukunna, to zuwa yanzu ka ga ana saka wakokin da na yi a kan zumunci da tarbiyyar yara da wani a kan watan Ramadan da sauran wakokin fadakarwa a gidan talabijin na Africa Tb3 da ke kasar Sudan wanda a sanadiyyar haka na samu kiraye-kiraye daga kasashen duniya da dama, baya ga sauran gidajen rediyo da muke da su da suka hada da Kada FM da Karama FM da Freedom FM da Gidan Rediyon Nagarta da Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da Gidan Rediyon Kwanni da ke Sakkwato da kuma Gidan Rediyon Muryar Jama’ar Jamus duk ana sanya wakokina, kazalika an sa ni a cikin wani shiri mai suna ‘Africa Magic’ a gidan talabijin na DSTb, sannan Situdiyo da bideo Club da na bude duk suna daga cikin ribar wakokin da nake yi ne.
Wane kira kake da shi ga mawaka ’yan uwanka da ’yan kasuwa?
Farko dai su sani cewa ita waka baiwa ce da Allah Yake bai wa wanda Ya so, kuma in Allah Ya ba ka, Yana so ne ka yi amfani da baiwar wajen yin abin da ya dace. Don haka kada mawaka su rika daukar baiwarsu suna amfani da ita ta inda ba ta dace ba, kan dan wani abin duniya, suna sanya batsa a wakokinsu ko zagin wadansu ko wasu abubuwa na bata tarbiyya suna watsa shi. Kuma da zarar an yi magana kan wata waka ko mai dauke da batsa ko bata tarbiyya sai ka ga jama’a na ta rubibi kuma ’yan kasuwa irin abin da suke so ke nan. Don haka kiran da zan yi musu shi ne su ji tsoron Allah su sani duk abin da mutun ya yi a duniya za a tambaye shi a Lahira ranar da masu daure maka gindi a nan ba za su iya kare ka a gaban Allah ba.
Ga gwamnati wacce sako kake da shi?
Ita kuma gwamnati muna kira a gare ta ta sani waka na daya daga cikin hanyoyin isar da sako da manufofin da gwamnati take so a yada shi a cikin al’umma. Kamar a nan Kudancin Kaduna muna da kungiyar mawaka da suka hada da Musulmi da Kirista, inda muke haduwa mu yi waka a kan zaman lafiya a ciki za ka ji ayoyin kur’ani da na Baibul da suka yi nuni kan zaman lafiya, to gwamnati ya kamata ta rika tallafa wa ire-iren wadannan wakoki da kuma su kansu mawakan don ci gaban kasa baki daya.