Dagaci ya kashe talakansa ya jefa gawarsa a rijiya

  An gurfanar da wani Dagaci a Jihar Neja a gaban kotun gargajiya da ke Minna kan zargin kashe talakansa da ya ake tsare da shi tare da jefa gawarsa a wata tsohuwar rijiya.   Bayanan ’yan sanda sun nuna cewa ana zargin Dagacin kauyen Madara da ke Karamar hukumar Kontagora a jihar, Malam Muhammed […]

Dagaci ya kashe talakansa ya jefa gawarsa a rijiya

 
An gurfanar da wani Dagaci a Jihar Neja a gaban kotun gargajiya da ke Minna kan zargin kashe talakansa da ya ake tsare da shi tare da jefa gawarsa a wata tsohuwar rijiya.
 
Bayanan ’yan sanda sun nuna cewa ana zargin Dagacin kauyen Madara da ke Karamar hukumar Kontagora a jihar, Malam Muhammed Sani, dan kimanin shekaru 50 a duniya da kashe Abbas Usman da yake tsare da shi a wani lokaci a watan Disemban shekarar da ta gabata.
 
Ana zarginsa da yin amfani da fatanya inda ya buga wa marigayin a kai inda hakan ya yi sanadin mutuwarsa nan take.