Dagaci ya shiga hannu kan daura auren budurwa mai ciki

Dagacin Kuka Yasku da ke Masarautar Gumel a Jihar Jigawa, Bulama Is’hak Kuka Yasku ya shiga hannun jami’an hukumar tsaro ta sibil difens, bisa zargin daura auren wata budurwa da ke dauke da juna biyu na wata bakwai.An kuma zargi dagacin da amsar Naira dubu 70 daga hannun wadanda ake zargi da yi wa budurwar […]

Dagaci ya shiga hannu kan daura auren budurwa mai ciki
Dagaci ya shiga hannu kan daura auren budurwa mai ciki

Dagacin Kuka Yasku da ke Masarautar Gumel a Jihar Jigawa, Bulama Is’hak Kuka Yasku ya shiga hannun jami’an hukumar tsaro ta sibil difens, bisa zargin daura auren wata budurwa da ke dauke da juna biyu na wata bakwai.
An kuma zargi dagacin da amsar Naira dubu 70 daga hannun wadanda ake zargi da yi wa budurwar ciki, inda ya ba wanda ya aure ta Naira dubu 20 a matsayin toshiyar baki.
Dagaci Bulama Is’hak ya tabbatar wa manema labarai da faruwar haka a gaban jami’an tsaro da suka gabatar da matasa 15 ciki har da dan dagacin mai suna Aminu Is’hak da ake zargi da yi wa budurwar ciki.
Ana zargin Dagacin da daura wa yarinyar (an sakaya sunanta) aure ne domin gudun bata wa dansa suna, wanda jami’an sibil difens suka gano ya shafe wata goma tare da budurwar.
Budurwar t ace samarin da suka yi lalata da ita su 17 ne, kuma sun sadu da ita sau 45, sai dai ba za ta iya gane wanda ya yi mata ciki daga cikinsu ba.
Dagacin ya ce sun so su yi rufa-rufa ne a kan lamarin, ya kuma ce sauran Naira dubu 50 da ya amsa daga wadanda ake tuhuma a matsayin tara da ya ce zai ba aka tursasa ya auri budurwar a matsayinbazawara da nufin in ta haihu ya yanka mata abin suna zai dawo wa hukuma ita.
Dagacin ya ce duk abin da ya yi bai sanar da Hakiminsa ba na Bosuwa ko masarautar Gumel kan lamarin ba.
Mahaifin budurwar, Malam Isah ya ce dora alhakin halin da ’yarsa ta shiga kan rabuwa da mahaifiyarta da suka yi shekara 10 da suka gabata. Ya ce yana yin duka abin da ya wajaba a kansa a matsayinsa na uba, inda ya nuna takaici kan halin da ta shiga tare da kira ga hukuma ta bi hakkin ’yarsa daga wurin wadanda suka yi lalata da ita.