Dagacin Abuja ya mutu a hannun ’yan bindiga
’Yan bindigar da suka sace dagacin kauyen Kikumi a yankin babban birnin tarayya Abuja, Surajo Ibrahim, sun ce ya mutu bayan wasu ‘yan kwanaki a hannunsu. Ishaku Madaki wani na kusa da basaraken ne ya tabbatar da rasuwar dagacin ga wakilinmu ta wayar tarho. Ya ce shugaban masu garkuwa da mutanen ne ya kira su […]
’Yan bindigar da suka sace dagacin kauyen Kikumi a yankin babban birnin tarayya Abuja, Surajo Ibrahim, sun ce ya mutu bayan wasu ‘yan kwanaki a hannunsu.
Ishaku Madaki wani na kusa da basaraken ne ya tabbatar da rasuwar dagacin ga wakilinmu ta wayar tarho.
Ya ce shugaban masu garkuwa da mutanen ne ya kira su ta waya da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ya sanar da su mutuwar.
Ya ce, dan ta’addar ya ce dole ne a biya kudin fansa Naira miliyan 6 domin kubutar da sauran mutane uku da suke hannu.
- Bankuna za su fara cirar 0.5% daga masu tura kudi ta intanet
- NAJERIYA A YAU: Abun Da Za A Fara Lura Kafin Shiga Tasi A Abuja
Madaki ya bayyana cewa kawo yanzu an yi karo-karo an bai wa ’yan bindigar Naira 300,000 daga cikin Naira miliyan 6 da suka bukata.
Zuwa yanzu dai ana dakon jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda a Abuja SP Adeh Josephine.
A baya, mun kawo muku rahoton cewa ’yan bindigar sun kai farmaki fadar dagacin, inda suka hallaka mutane uku, suka kuma yi awon gaba da basaraken da wasu mutanen kauyen uku.