Dage kasuwa zuwa Abiele ya samar da cigaba ga ’yan kasuwa –Shugaba Abdulrazak

Shugaban kasuwar shanu Abiele, cikin karamar Hukumar Etsako ta Yamma, Alhaji Abdulrazak Umar ya bayyana dalilan da ya sa suka dage kasuwar shanu daga Auchi ta koma garin Abiele, kimanin shekara biyar yanzu.Alhaji Abdulrazak ya yi bayanin ne a wata zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar kwanan baya, inda ya ce dage […]

Dage kasuwa zuwa Abiele ya samar da cigaba ga ’yan kasuwa –Shugaba Abdulrazak

Shugaba Alhaji Abdulrazaqu UmarShugaban kasuwar shanu Abiele, cikin karamar Hukumar Etsako ta Yamma, Alhaji Abdulrazak Umar ya bayyana dalilan da ya sa suka dage kasuwar shanu daga Auchi ta koma garin Abiele, kimanin shekara biyar yanzu.
Alhaji Abdulrazak ya yi bayanin ne a wata zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke kasuwar kwanan baya, inda ya ce dage kasuwar ya zama dole saboda ainihin inda take a Auchi, tana cikin wani lungu ne.  “’Yan kasuwanmu suna nuna damuwarsu da fargaba da kasancewar kasuwar  a wurin kuma babu wani cigaba da muka samu na a-zo-a-gani duk tsawon zaman da muka yi a wurin. Wannan ya sa muka yanke shawarar tashinta zuwa garin Abiele kuma, alhamdu lillahi, tunda muka koma, komai namu yana tafiya daidai. Mun samu ci gaba kwarai ta fuskar kasuwar da zaman lafiya tsakanin mu ’yan kasuwa da kuma sauran jama’ar “. Inji shi.
A karshe ya shawarci ’yan kasuwar da su kara yin hakuri da juna kuma su bi dokar kasa, su kauce wa tayar da duk fitina, saboda a sami karuwar zaman lafiya, wadda ita ce tushen arziki da cigaban jama’a.