Dage zabe: Jonathan yana tsoron Buhari – Jaridar New York Times

Rashin taka rawar gani a shekara shida na mulkin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne yake kara ba abokin adawarsa Janar Muhammadu Buhari dama ta lashe zaben watan gobe. Jaridar New York Times da ake bugawa a Amurka ne ta bayyana haka a ra’ayinta na ranar Litinin da ta gabata mai taken: “Mugun zabin da ke […]

Dage zabe: Jonathan yana tsoron Buhari – Jaridar New York Times
Dage zabe: Jonathan yana tsoron Buhari – Jaridar New York Times

Rashin taka rawar gani a shekara shida na mulkin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne yake kara ba abokin adawarsa Janar Muhammadu Buhari dama ta lashe zaben watan gobe.

Jaridar New York Times da ake bugawa a Amurka ne ta bayyana haka a ra’ayinta na ranar Litinin da ta gabata mai taken: “Mugun zabin da ke gabanNajeriya,” inda ta ce muguwar gazawar Jonathan ne ta taimaka wajen kara farin jinin Buhari a tsakanin ’yan Najeriya.
Jaridar ta ce, a zaben Shugaban kasa na 28 ga Maris, “An bar masu kada kuri’a da zabin ko dai ci gaba da rike lusarin Shugaban kasa ko dawo da dan mulkin kama-karya na zamanin soja.”
Ra’ayin jaridar ya ce, Buhari “Alamu sun nuna Buhari zai lashe zaben fiye da Mista Jonathan wanda ya yi muguwar gazawa a fagen mulki idan aka lura da karbuwar tsohon Shugaban mulkin sojan.”
Dangane da dage zaben, jaridar New York Times ta ce, “Ana iya amincewa da da duk wata hujja da gwamnatin Shugaba Jonathan ba ta bata lokacinta a shekarar da ta gabata tana nuna babu wata matsala da mayakan Boko Haram za su iya haifarwa a zaben, kuma idan akwai wani abu da ake gani na rashin karfin sojin Najeriya za a iya inganta shi cikin ’yan makonni.”
‎Ta ce “Ya bayyana cewa akwai yiwuwar Mista Jonathan ya damu da irin karbuwar Muhammdu Buhari, wani tsohon Shugaban mulkin soja wanda ya sha alwashin murkushe Boko Haram.”
Jaridar ta ce ta hanyar dage zaben Jonathan yana kokarin tatuke asusun babban abokin adawarsa, yayin da shi kuma zai yi ta amfani da dukiyar gwamnati wajen ci gaba da kamfe dinsa.
Jaridar ta ce, sacewa da kai hare-hare da kungiyar ke kaiwa ya nuna rashin karfin sojojin Najeriya da kuma rashin katabus din gwamnati.
Sharhin jaridar ya kara da cewa: “Duk da cewa gwamnatin Jonathan a baya ba ta nuna sha’awa ba, a wani lokacin ma tana dakile yunkurin Amurka da kasashen Turai na tallafa mata kan lamarin, daga baya ya rika dada nuna damuwa.”
A karkashin mulkin Jonathan baya ga rashin tsaro an samu gagarumar cin hanci da rashawa da kuma gazawar gwamnati na fadada harkokin tattalin arzikinta a daidai lokacin da farashin man fetur ke muguwar faduwa, “Lamarin da ya sa ’yan Najeriya su fara nemo wani sabon Shugaban kasa,” inji jaridar.
Jaridar ta karkare da cewa, duk da Najeriya ba za ta iya lamuntar tashin hankalin zabe ba, “Akwai yiwuwar hukumomin tsaro ba za su iya kare wasu sassa a ranar zaben ba. Amma dage zaben yana iya jawo karin barazanar rashin tsaro fiye da baya,” inji jaridar.