Dage zabe: PDP ta gano ba ta da nasara ne – Hassan Yusuf

Tsohon dan takarar Shugaban kasa a Jamhuriyya ta Biyu a rusasshiyar Jam’iyyar PRP Halifa Hassan Yusuf ya ce dage zaben kasar nan zuwa mako shoda da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi alama ce ta ruwa ya kare wa dan kada, domin abin da ba a yi shi cikin shekara biyar ba, ba za […]

Dage zabe: PDP ta gano ba ta da nasara ne – Hassan Yusuf
Dage zabe: PDP ta gano ba ta da nasara ne – Hassan Yusuf

Tsohon dan takarar Shugaban kasa a Jamhuriyya ta Biyu a rusasshiyar Jam’iyyar PRP Halifa Hassan Yusuf ya ce dage zaben kasar nan zuwa mako shoda da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi alama ce ta ruwa ya kare wa dan kada, domin abin da ba a yi shi cikin shekara biyar ba, ba za a yi shi a mako shida ba.
Halifa Hassan Yusuf wanda har wa yau shi ne Galadiman Damaturu ya shaida wa Aminiya cewa dage zaben bai zo da mamaki ba, domin alamu sun nuna akwai kullalliyar yin haka tun lokacin da Mai ba Shugaban kasa shawara kan Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki ya nemi hukumar zaben ta dage zaben zuwa gaba.
“Tun a wancan lokaci al’ummar Najeriya suka sha jinin jikinsu cewa akwai wata a kasa, domin Jam’iyyar PDP ta gano ba ta da nasara, shi ya sa take kokarin yin wasu dabaru ko za su fisshe ta, sun manta da cutar mutuwa ba ta da magani,” inji shi.
Ya kara da cewa, gwamnati ta ce cikin mako shida tana kyautata zaton samun galaba a fadan da take yi da ’yan Boko Haram, ya ce in har ya kasance lallai zargin da jama’a ke yi cewa da hannun gwamnati a ciki ya tabbata ke nan, “domin a baya al’umma sun zargi gwamnati dangane da kasa shawo kan rikicin duk da dokar ta baci da ta sa wa jihohin Yobe da Borno da Adamawa,” inji shi.
Galadiman na Damaturu ya ce dage zaben da Shugaban Hukumar INEC ya yi abin bakin ciki ne domin hakan wani yunkuri ne na tilasa mulki irin na kama-karya ga al’ummar kasar nan.
Halifa Hassan Yusuf, ya ce lallai shugabannin kasar nan su san cewa canjin da suke ki sai ya tabbata, domin idanuwan al’ummar duniya na kansu.