dage zabe: Wani dattijo ya yanke jiki ya fadi ya mutu a Borno

Wani dattijo mai shekara 73, ya yanke jiki ya fadi ya rasu sakamakon dage zabe da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi a ranar Asabar da ta gabata.Marigayin mai suna Malam Muhammadu da ke Unguwar Ngomari Kwastin a cikin birnin Maiduguri, ya yanke jiki ne ya fadi a lokacin da wani ya kawo masa […]

dage zabe: Wani dattijo ya yanke jiki ya fadi ya mutu a Borno
dage zabe: Wani dattijo ya yanke jiki ya fadi ya mutu a Borno

Wani dattijo mai shekara 73, ya yanke jiki ya fadi ya rasu sakamakon dage zabe da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi a ranar Asabar da ta gabata.
Marigayin mai suna Malam Muhammadu da ke Unguwar Ngomari Kwastin a cikin birnin Maiduguri, ya yanke jiki ne ya fadi a lokacin da wani ya kawo masa labarin cewa ya ji a rediyo cewa Hukumar Zabe ta dage zaben da za a gudanar a gobe Asabar.
daya daga cikin ’ya’yansa mai suna Malam Sani ya tabbatar wa  wakilinmu haka a garin Maiduguri, inda ya ce “dage zaben nan da Hukumar INEC ta yi ba mu ji dadinsa ba ya haifar mana da mugun yanayi, mun kwallafa rai cewa za a samu canji a wannan lokaci, to, amma sai abin ya zame mana bakin ciki, saboda daga cewa an dage zaben sai mahaifinmu ya yanke jiki ya fadi, mun dauke shi muka yi ta yi masa fifita daga muka dauke shi muka kai shi asibiti da likitoci suka duba shi sai suka ce hawan jini ne, wani ya ce ciwon zuciya ne.”
Malam Sani ya ce tunda mahaifinsu ya fadi har suka kai shi asibiti ba ya cin abinci ba ya shan abin sha kuma ba ya magana har tsawon kwana biyun da ya yi kafin ya rasu, “Don haka ni da ’yan uwana mun tabbata cewa bakin cikin samun labarin dage zabe ne ya sa shi hawan jini har ya kai ga ajalinsa,” inji shi.
“Ni kaina na kasa cin abinci daga lokacin da aka dage zaben har zuwa lokacin da mahaifinmu ya rasu don haka wannan dage zabe bai yi mana dadi ba,” inji Sani.
Ya ce, sakamakon yadda al’amura suka tabarbare mahaifinsu ya sha tara su yana yi musu bayani cewa lallai idan zabe ya zo, dukkansu su zabi Jam’iyyar APC, ko za a samu canjin gwamnati ta yadda bayansa za ta yi kyau ko bayan ransa.
 Malam Sani ya ce mahaifinsu bai taba aikin gwamnati ba, kuma ba dan siyasa ba ne sana’arsa tukin mota ne har zuwa lokacin da girma ya hana shi, kuma ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya takwas.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ce Shugaban Hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega ya sanar da dage zaben Shugaban kasa da na majalisun kasa da na gwamnoni da aka shirya za a gudanar a gobe Asabar da kuma ranar 18 ga wannan wata na Fabrairu, zuwa ranar 28 ga watan Maris da kuma 11 ga watan Afrilu.

…Jama’atu da ACF sun bukaci jama’a su ci gaba da addu’a

Daga Mohammad Yaba, Kaduna

kungiyar Kare Maradun Arewa (ACF) da kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) sun yi Allah wadai da dage babban zabe da Hukumar Zabe ta kasa ta yi bisa dalilin tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
kungiyoyin biyu sun kuma bukaci ’yan Najeriya su yi hakuri tare da rungumar kaddara a kan abin da ya faru.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ACF ta raba wa manema labarai dauke da sa hannun Kakakinta Muhammadu Ibrahim ta bukaci ’yan Najeriya su cigaba da addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
“Mun yaba wa ’yan Najeriya saboda hakurin da suka nuna kan abin da ya faru a cikin wannan yanayi na rashin tabbas da ya mamaye kasar nan. Akwai bukatar ’yan Najeriya su ci gaba da addu’a su kuma kara hakuri tare da kauce wa duk abin da ka iya jawo karya doka da oda. Saboda yin haka zai kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a kasar nan, musamman na tabbatar da zabe mai inganci. Jajircewarmu ga tabbataccen tsarin dimokuraddiya ne kawai zai kara mana hadin kai da zama lafiya da juna,” inji sanarwar.
Ita kuwa Jama’atu Nasril Islam baya ga nuna bacin rai kan dage zaben ta yi kira ga ’yan siyasa su guji yin kalaman batanci da ka iya kawo rikici a kasar nan musamman idan suka yi la’akari da irin damuwar da ke cikin zukatan jama’a.
Jama’atu ta bayyana haka ne a wata sanarwa da Babban Sakatarenta na kasa, Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya raba wa manema labarai a Kaduna.
Ta yi kira ga jama’a su ci gaba da hakuri domin sabuwar ranar zaben da aka sanya za ta zo ta wuce lafiya.
“Damuwarmu ita ce a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a kuma muna fata shugabannin hukumomin tsaro za su taimaka matuka a wannan sashi,” inji shi.
Daga nan Jama’atu ta tunatar da ’yan Najeriya bukatar da ke akwai ta su ci gaba da gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya.