dage zabe ya janyo faduwar darajar Naira da hannayen jari
Darajar Naira da farashin hannayen jari sun fadi a kasuwar canji da kasuwar hannayen jari da bankuna a farkon makon da muke ciki sakamakon dage zaben da hukumar INEC ta yi a makon da ya jiya.Hukumar INEC ta bayyana cewa ta dage zabe daga ranar 14 da 28 ga watan Fabarairu zuwa ranar 28 ga […]
Darajar Naira da farashin hannayen jari sun fadi a kasuwar canji da kasuwar hannayen jari da bankuna a farkon makon da muke ciki sakamakon dage zaben da hukumar INEC ta yi a makon da ya jiya.
Hukumar INEC ta bayyana cewa ta dage zabe daga ranar 14 da 28 ga watan Fabarairu zuwa ranar 28 ga watan Maris da ranar 11 ga watan Afrilu.
dage zaben ya janyo kasuwar canji ta shiga rudu inda kudaden kasashen waje musamman ma Dalar Amurka ta yi karanci a kasuwanin can da bankuna.
Wani mai harkar canji, Alhaji Musa Muhammadu ya shaida wa Aminiya cewa daga ranar da hukumar INEC ta bayyana dage zabe Dala ta yi karanci. “Tun daga ranar Dala ta yi karanci. Idan ka je banki ma sai su ce maka ba su da Dala. To ka ga dole darajar Naira ta ci gaba da faduwa saboda karancin Dala. Duk wanda yake da Dala sai ya kara mata kudi saboda ya san duk farashin da ya sanya za a saya saboda ana mutukar bukatarta.” Inji shi.
Aminiya ta gano cewa a karshen makon jiya farashin Naira ya yi kasa duk da matakan da Babban Bankin Najeriya ya dauka.
Sai dai duk da haka masu lura da al’amuran yau da kullum sun yi hasashen idan Babban Bankin Najeriya bai dauki matakan da suka dace ba Naira za ta ci gaba faduwa.
Hakzalika farashin hannayen jari sun fadi inda hada-hadar hannayen jarin da aka yi a kasuwar hannayen jari ta Legas suka yi kasa da Naira biliyan 208.
A lokacin da aka kada kararrawar karshe ta rufe kasuwar hannayen jari a Legas kasuwar ta bude da jarin fiye da tiriliyan 10 amma aka samu ragin fiye da kashi biyu inda kasuwar ta rufe da jarin tiriliyan 9 da digo 797.