dage zabe ya kawo cikas a harkokin kasuwacin Kuros Riba

karancin ’yan Arewa mazauna Jihar Kuros Riba da ke kasuwanci ya kawo cikas da rashin ciniki, tun daga lokacin da zabe ya karato, inda ’yan Arewa suka rika tafiya gida zuwa jihohin su na asali, domin yin zabe kafin daga bisani hukumar zabe ta bayar da sanarwar dage zaben, har sai ranar 28 ga Maris. […]

dage zabe ya kawo cikas a harkokin kasuwacin Kuros Riba
dage zabe ya kawo cikas a harkokin kasuwacin Kuros Riba

karancin ’yan Arewa mazauna Jihar Kuros Riba da ke kasuwanci ya kawo cikas da rashin ciniki, tun daga lokacin da zabe ya karato, inda ’yan Arewa suka rika tafiya gida zuwa jihohin su na asali, domin yin zabe kafin daga bisani hukumar zabe ta bayar da sanarwar dage zaben, har sai ranar 28 ga Maris. Harkokin kasuwanci a Jihar Kuros Riba da ’yan Arewa mazauna babban birnin jihar, Kalaba , ke yi ya hadu da cikas, na rashin ciniki, inda wasu daga cikin ’yan kasuwar da Aminiya ta tattauna da su suka yi wa wakilin mu bayani .

Alhaji Malami kofar Atiku Sakkwato, dan kasuwa mazaunin Kalaba da ke sana’ar sayar da albasa, ya bayyana cewa “bisa hakikanin gaskiya yanayin ciniki a kasuwar mu ta albasa ya canja, tunda yanzu idan aka kwatanta shi da kafin lokacin da ’yan uwan mu, ’yan Arewa ke nan Kalaba kafin a dage zabe, domin wasu duk sun tafi gida yin zabe, amma abu ne wanda ya shafi ko ina a cikin Najeriya.”
Ya ce yana ganin sauyawar akalar ciniki na kasuwanci “abu ne kamar daga yanayi na gwamnati, saboda tsuke bakin aljihu da aka yi, wasu jihohi suna kukan ba a biya albashi ba, wasu kuwa suna kuka ne da rashin kwanciyar hankali.”
Sai dai kuma wani korafi da dan kasuwar ya yi dangane da sana’ar tasu ta albasa, ita ce “ko nan ma Kuros Riba matsalar rashin biyan albashin ce ta sanya abokan huldar mu suke kokawa a kai, amma duk da haka a kasuwar daga cikin kashi uku ana samun kashi biyu na cinikin kashi guda ne muke ganin ya tafi. Tun farko an rika yada jita-jitar cewa, saboda zabe da za a yi ne na rashin tabbas a tsaron lafiya da kuma dukiyoyin jama’a ne ya sanya ’yan Arewa, musamman wadanda ke kawo albasa jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba da kuma Ribas daga sassan jihohin Sakkwato da Kebbi sun kaurace wa Kudanci, sakamakon ba su san abin da hanya za ta haifar ba, idan sun dauko kaya kafin su iso Kudu. Lamarin da ya haifar da karancin kayan miya, wadanda suka had ada dangin tumatiri da albasa da kayan rafi, amma duk da haka Alhaji Malami Sakkwato, daya daga cikin ’yan kasuwar, ya bayyana cewa: “Ba haka ba ne su ma ’yan yankin Kuros Riba ai suna tafiya Arewa sawo kayan, amma tsoron yadda kasuwar za ta kaya ce saboda rashin ciniki ba ta tsaro ba ce.”
Ya ce kafin ’yan Arewa mazauna Kalaba su tafi Arewa, domin yin zabe, ana sayar da kowane buhun albasa Naira dubu 23, amma yanzu ana sayar da shi kan farashin Naira dubu 20. karshe ya yi kira ga ’yan uwan da suka tafi gida domin yin zabe, tunda an yi karin kwanakin, to, su dawo su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin su. “Insha Allahu babu wata matsala ko wani abu da zai faru,” inji shi
A layin Bagobiri, unguwar Hausawa, nan kuma Aminiya ta yi kacibis da Hadiza Salihu, mai tuyar masa, inda ta yi bayani yadda tafiya gida da kwastomominta suka yi ke shafar harkar kasuwancinta. “Cinikin dai babu laifi, ana kai, sai dai an samu koma baya a cinikin, domin kafin mutane su tafi gida idan na yi masa ina cikin Naira dubu 13 kullum, amma yanzu da kyar nake iya hada Naira dubu 10. Duk da halin karancin ciniki da ake fama da shi na samu biyan bukata a wannan sana’a.” inji ta.
Shi ma Abdullahi Garba Saminaka, wani matashi ne da ke sana’ar cajin batirin waya da sayar da kati, ya yi wa Aminiya bayanin yadda karancin abokan mu’amala ya shafi sana’arsa, inda ya ce, sai godiya. “Ta bangaren sana’ata duk kwastomomin da muke mu’amala da su duk sun tafi gida, su yi zabe. A yanzu muna maneji, muna samun na abinci dan daidai da za a yi bukatu, amma ba kamar da ba.