Dahiru Tsoho: Makahon da ke haka rijiyar da ta gagari masu ido

Aminiya: Sai ka gabatar da kanka?dahiru tsoho: Sunana dahiru Musa, sai dai ana mini lakabi da dahiru Tsoho, asalinmu mutanen kasar Nijar ne, daga kauyen Gagama da ke jihar Maradi, aiki ne ya kawo mahaifinmu kasar nan kuma in banda yarmu babba, gaba dayan ’ya’yansa a nan Suleja ya haife mu a Unguwar Iya, daga […]

Dahiru Tsoho: Makahon da ke haka rijiyar da ta gagari masu ido
Dahiru Tsoho: Makahon da ke haka rijiyar da ta gagari masu ido

Aminiya: Sai ka gabatar da kanka?
dahiru tsoho: Sunana dahiru Musa, sai dai ana mini lakabi da dahiru Tsoho, asalinmu mutanen kasar Nijar ne, daga kauyen Gagama da ke jihar Maradi, aiki ne ya kawo mahaifinmu kasar nan kuma in banda yarmu babba, gaba dayan ’ya’yansa a nan Suleja ya haife mu a Unguwar Iya, daga baya ne muka dawo nan Pangamu inda ya gina gida.
Aminiya: Mai ya ba ka sha’awar shiga sana’ar fasa dutsi da hakar rijiya?
dahiru Tsoho: Ganin zaman banza da na ke yi ni, sai na ce bari in fara yinta, idan mahaifinmu ya fita da safe sai in rika yi, in na tara kamar baro guda na dutse sai in sayar Naira dari. Ana nan har na shiga tara kamar tifa, to da yake mahaifina sana’ar lodin tifa yake yi, sai hakan ya taimake ni wajen sayar da dutsen cikin sauki idan ya taru, shi kansa ya yaba abun, ya ce na saukake masa aiki, yanzu sai dai ya ji da kannena.
Aminiya: wannan larura ta makanta daga baya ne ta same ka ko dama da ita aka haife ka?
Aminiya: Daga baya ne ta same ni a lokacin ina da shekara kamar 15, kuma lalurar makantar ce ma ta karfafa min gwiwa na fara yin sana’ar, kasancewar ina zaune haka nan a gida, to idan mahaifina ya fita aiki ni kuma sai in hau fasa dutse, kasancewar Unguwar tamu kusan dutse ne ta ko-ina a lokacin. Ita wannan makanta ciwon bakon dauro ne ya same ni da ni da kannena biyu, an kaimu asibiti, shi gudan ya warke ba tare da wata nakasa ba, ni kuma na samu sauki sai dai ban iya gani abu daga nesa da kyau, sai dai in rika ganin hazo-hazo, to sai wani abokin mahaifinmu ya ce idan aka sa ruwan farar albasa a idon zan warke, sai dai ana sawa sai idona guda ya tsiyaye, dayan kuma bai tsiyaye ba amma sai na daina gani, ka san albasa tana da zafi, bare kuma fara, to daga baya ne sai ya ce ai shi yana nufin za a shafa ruwan albasan ne a tsumma. Ita daya ’yar uwar tawa kuma bakon dauron ya yi ajalinta Allah Ya yi mata cikawa.
Aminiya: Ya aka yi ka fada sana’ar hakar jiya?
dahiru Tsoho: Sana’ar hakar rijiya daga gidanmu na fara, ana wahalar ruwa, mu kuma gidanmu ba wata rijiya da ke kusa da mu, sai kawai na dubi tsakiyar gidan na fara haka, da mahaifinmu ya dawo ya tambaya wannan ramin fa, mahaifiyarmu ta yi masa bayani, sai ya ce to Allah Ya sa a dace. Haka na rika yi, a ranar da a ka cika mako guda sai ga ruwa, amma sai na ci karo da dutsi, sai na dauko guduma da cisil ina balle dutsen sai ga ruwa har ya kawo ni ga gwiwa, aka zuro min bokiti na jefa shi ciki aka fito da dutsen, ni kuma na sa kafa gefe da gefe na fito. To daga nan kuma sai aka rika nemana da aikin haka rijiya. Wata rijiyar wadansu ne suka fara hakarta amma idan aka yi karo da dutse sai a neme ni, haka nan ina hakar salga. Ba na mancewa akwai wata rijiya da wadansu suka haka amma sai suka cim ma babban dutse bayan sun fara samun ruwa, nan suka watsar da aikin, mai gidan ya nemo wadansu masu fasa dutse, sun yi iya kokarinsu amma su ma suka bar aikin, to a nan aka kwatanta masa inda nake, ya zo ya same ni, na tambaye shi launin dutsen ya ce farin dutse ne, na ce masa zai fasu. Na yi kamar mako guda ina aikin, har na isa inda ruwa yake da wadata, ya mini kyakkyawar sallama na dawo. Bayan wannan na yi wani irinsa a yankin Kwamba Suleja. wadanda suka fara aikin sun wahala sosai saboda dutsen ya yi ta yankarsu, sai suka watsar, da na je wajen sai mai gidan ya ce da abokin aikina sai ya fara shiga ya duba, sai ya ce ina? ai ni ne jagora ni ke fara shiga, nan mai gidan ya cika da mamaki, na shiga na shafa dutsen, na fito na ce masa zai fasu amma sai mu yi ciniki tukuna, muka shirya, mun fara aikin a ranar Asabar washegari Lahadi muka kammala aikin.
Aminiya: Kamar wadanne nau’ukan duwatsu ka sani a wannan aiki?
dahiru Tsoho: Akwai farin dutse, akwai bakin dutse, wanda muke kunna masa wuta, akwai kuma wani mai gari kamar na siminti, akwai kuma mai kamar launin ja, ni ban sansu ba a ido, amma ina gane su idan na shafa su, wani dutsen idan muna aikinsa a kullum sai mun kai kayan aikinmu kuda kafin mu ci gaba da aiki. Muna kuma aikin ne da kayan aiki kamar kwalba da Cisul da kuma Guduma.
Aminiya: Wane irin kalubale ne za ka ce ka ke fuskanta a wannar sana’a?
dahiru Tsoho: Babban kalubale da nake fuskanta ita ce wannar sana’a ce na dan wani lokaci, wannan lokaci shi ne lokacin zafi da ake karancin ruwa, ko masu bukatar sabon rijiya ne son fi son a yi masu aiki a wannan lokaci don tabbatar da cewa inda aka samu ruwan nan an samu ke nan. Sai kuma wajen ba mu hakkinmu, mun fi son a ba mu wani abu a kullum idan muka yi aiki, saboda shi wannan aiki sai da ruwan ciki ne za a ja na rijiya, amma wasu sai su ce sam sai an kai karshe. Ba ni mancewa irin haka ta hada ni da wani, nan na bar masa aikin ba tare da na karbi kudin aikin yinin ba, a karshe haka mu ka bar aikin bai kuma samu wani ba sai dai aka cike rijiyar haka nan. To a dalilin irin hakan muka daina aikin jinga na gaba daya, sai dai mu rika karbar na yini kawai, don ba mu san iya dutsen da za mu samu ba kafin mu kai ga ruwa.
Aminiya: Wane irin alheri ne kuma za ka ce wannan sana’a ta yi maka?
dahiru tsoho: A gaskiya wannan sana’a ta yi min goma na arziki, na farko dai ta hana ni bara, kuma a cikinta na yi aure, yau a na neman shekara biyu ke nan, kuma kasancewar mahaifina ya rasu, yau wajen shekara goma sha hudu ke nan, ni ke kula da kanwata da kuma kani, haka nan ita mahaifiyarmu, wadda Allah Ya yi mata rasuwa a shekarar da ta wuce.