Dahuwar kabeji mai nama
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya ba mu ikon tarbiyyantar da su yadda ya kamata. A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama, yawan girka abinci iri daya na ginsar yara da maigida. A kullum mutum yana […]
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya ba mu ikon tarbiyyantar da su yadda ya kamata. A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama, yawan girka abinci iri daya na ginsar yara da maigida. A kullum mutum yana son cin sabon girki. Don haka dole ne mata a dage wajen koyon nau’o’in girke-girke domin kayyatar da abincin da ake dafawa a gida.
Abubuwan da za a bukata
- Nikakken danyen nama
- kabeji
- Attarugu
- Koren tattasai
- Albasa
- Magi
- Karas
- Kori
- Citta
- Tafarnuwa
- Man gyada
Hadi
A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon minti biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe.
A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken naman a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai a yi ta gaurayawa har sai naman ya nuna ya soyu sannan a kwashe.
A sami kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sai a debo hadin nama a zuba a ciki sannan a yi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen.
Sai a dora tukunya a kan wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe,
Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abin karyawa.