Daidaito da bambanci a tsakanin namiji da mace

Akwai daidaito na adalci da mu’amalar al’umma a tsakanin maza da mata, sannan akwai bambance-bambance halitta da dabi’a a tsakanin jinsi. Don haka a duk lokacin da ake magana a kan bambance-bambancen da ke tsakanin namiji da mace, to ana magane ne akan bambancin da tsarin halitta ya haifar ba wai don wani jinsin ya […]

Daidaito da bambanci a tsakanin namiji da mace
Daidaito da bambanci a tsakanin namiji da mace

Akwai daidaito na adalci da mu’amalar al’umma a tsakanin maza da mata, sannan akwai bambance-bambance halitta da dabi’a a tsakanin jinsi. Don haka a duk lokacin da ake magana a kan bambance-bambancen da ke tsakanin namiji da mace, to ana magane ne akan bambancin da tsarin halitta ya haifar ba wai don wani jinsin ya fi wani jinsin ba, halitta ce ta samar da haka. Wannan ne ya sa suke zama tare, ba tare da sun gaji da juna ba, kuma halittarsa ce ta dora wa kowanne nauyin da yafi dacewa da shi. 

Don haka, ga abinda masana halayyar dan Adam, da Malamai, da kuma likioci suka bayyana dangane da bambancin da ke tsakaninsu, don a fahimci yanayinsu da kuma irin rawar da kowannensu zai iya takawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
A tsarin halitta, idan muka dauki girman jiki da tsawo; mafi yawan mata kanana jiki ne da su, maza kuma sun fi girman jiki; yawancin mata gajeru ne akan maza. Sautin muryar namiji tana da girma, ita kuma mace muryarta siririya ce; mace ta fi namiji saurin girma, domin tun tana cikin mahaifa zuwa waje mace ta fi garkuwar kamuwa da cututtuka. Mace tana riga namiji saurin balaga, kuma tana riga namiji daina haihuwa. Huhun namiji ya fi na mace zukar Iska. Haka nan ita kanta kwakwalwa ta namiji ya fi na mace zukar iska. Haka nan ita kanta kwakwalwa ta namiji ta fi ta mace girma. Zuciyar namiji ta fi saurin bugawa akan ta mace.
A halayya kuma masana sun yi ammana cewa, namiji ya fi mace son aikin karfi, da gwagwarmaya, mace kuwa ta fi son tafiyar da komai a hankali. Mace ba ta iya yanke shawara a gurguje, kamar yadda namiji kan yanke nan take. Wannan dalili ne ya sa da wuya ka ji mace ta rataye kanta, ita ta gwammace ta sha guba, ko wani magani da zai hallakata nan take, wanda bai taka kara ya karya ba, shi kuwa namiji hakan bai zame abin a zo, a gani a wajensa ba.
Mace ta fi son kwalliya da duk wani abin da zai kayatar da ita, fiye da namiji, haka nan mace ta fi namiji surutu, kuma ta fi namiji kula da yara; ita hankalinta a kullum akan ci gaban iyali ya ke, kuma ita mace ba ta iya boye sirri kamar yadda namiji yake boyewa. Mace ta fi namiji saurin kuka, ta yadda za ka ga cewa abu kadan zai iya sanya mace kuka.
A fannin zamantakewa, masana sun ci gaba da cewa sha’awa ce ke sa namiji son mace, amma shi namiji muhimmancinsa ne ke sa mace sonsa. Burin namiji shi ne ya samu macen da zai iya iko da ita, ita kuwa a kullum so take ta samu mai kaunarta. Mace ta fi son ganin jarumtar namiji, shi kuwa kwalliya da kyawun mace su ne a gabansa. Duk matsayin da mace take ciki tana iya boye son tarawa fiye da namiji.
Bincike ya tabbatar da cewa da a ce mace tana da kamannin irin na namiji da halayyar irin ta sa, da ba zai iya ba shi sha’awar da zai ja ta gare shi ba, ballantana ma har su iya zama tare su yi mu’amala irin ta auratayya tare ba.
A fannin kula da lafiya, mata sun fi kula da lafiyar jikinsu da ta iyali, musamman ’ya’yansu kanana, amma namiji sai ciwo ya ci, ya cinye sannan yake tafiya asibiti. Sai dai duk da haka mace ta fi laulayi, ta yiwu saboda al’ada da haihuwa da shayarwa da rainon ’ya’ya. Allah Shi ne Masani akan kowane al’amari. Mu dai neman dace muke yi, ta yadda za a kyautata danganta a tsakanin jinsi, a fahimci juna, don ci gaban al’umma a kowane fanni na rayuwa.
Na binciko wadanann bambance-bambance ce ne don a fahimci yanayin kowa da kuma irin rawar da kowannensu zai iya takawa. Saura da me? Allah S.W.T yana cewa a cikin alkur’ani “Ba mu halicci mutum da aljani ba sai don su bauta masa” ka ga ke nan, akwai matukar bukatar mu kyautata alakar da ke tsakain namiji da mace, musamman ma a zamantakewar aure, domin gyaruwarta shi ne gyaruwar al’umma. Allah ya agaza mana.

Marubucin Ibrahim Hamisu za a iya tuntubarsa ta hanyoyin sadarwa kamar haka:
080 60651676: Email: [email protected]

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu