Daidaiton mata da maza ba mai yiwuwa ba ne – Nafisa Gurori
Malama Nafisa Adamu Gurori, lakcara ce a Jami’ar Jihar Sakkwato, kuma yanzu haka tana karatun digirinta na uku a fannin Nazarin Addinin Musulunci. Mace ce mai saukin kai da son jama’a su dogara da kansu; musamman mata. Aminiya ta tattauna da ita domin sanin tarihin rayuwarta da sauran batutuwan da suka shafi mata: Tarihina Sunana […]
Malama Nafisa Adamu Gurori, lakcara ce a Jami’ar Jihar Sakkwato, kuma yanzu haka tana karatun digirinta na uku a fannin Nazarin Addinin Musulunci. Mace ce mai saukin kai da son jama’a su dogara da kansu; musamman mata. Aminiya ta tattauna da ita domin sanin tarihin rayuwarta da sauran batutuwan da suka shafi mata:
Tarihina
Sunana Nafisa Adamu Gurori, an haife ni a ranar 23 ga Yunin 1981 a cikin Unguwar Difilomat da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu a birnin Sakkwato. Na shiga makarantar firamare kan Titin Dorowa a Unguwar Low Cost na kare a 1992, sai na tafi Kwalejin ’Yan mata (GGC) ta Jihar Sakkwato, ita ma na kammala a 1998. Ina cikin dalibai masu hazaka da aka bai wa Jarrabawar Shiga Jami’a wato (JAMB) na rubuta jarrabawar na samu sakamako mai kyau, amma mahaifina ya ce sai na yi aure zan ci gaba da karatu, idan mijina ya aminta. Daga nan ne mahaifiyata ta tura ni Jihar Legas wurin dan uwanta domin in koyi yadda ake rayuwar aure, in na zauna gidan mahaifina ba zan samu damar koyo ba, bayan ma’aikatan da muke da su aikin gidan ya fi karfina, a haka na zauna can. Na koma Abuja, daga bisani na dawo gida lokacin da wani dan uwana ya ce yana son zai aure ni, mun yi auren a shekarar 2001 da shi, sunansa Dokta Suleiman Abubakar, har zuwa 2013 Allah ya kawo kaddarar rabuwa, ida ya koma kasar Uganda da zama. Mun haifi ’ya’ya shida a tsakaninmu maza biyar mace daya.
A lokacin da nake da aure a haihuwan fari na koma jami’a, inda na yi digirin farko a fannin Nazarin Addinin Musulunci. A nan na yi digiri na biyu, ina kuma sana’o’in mata na cikin gida. A wurin mahaifina ni ce ta uku ina da kanne 31 mu 34 ne a gidanmu.
Yanzu haka ina karatun digiri na uku, kuma ina shekara ta uku. Ina rubutu kan hakkin mata domin fadakar da su mene ne yake gyaran aure, ladabi da biyaya ne kawai ke rikon aure.
Ina cikin kungiyoyin mata na addini daban-daban. Kafin in fara karantarwa a Jami’ar Jihar Sakkwato na yi karantarwa a Kwalejin ’Yan mata ta Tarayya (FGC) da ke nan Sakkwato.
Kalubalen da na fuskanta
Babban kalubalena shi ne mutuwar aurena – domin mutuwar aure ba abu ne mai sauki ga kowace mace ba. Na yi bakin ciki na shiga yanayin da ya so taba rayuwata ganin rana guda mijina ya tafi ya bar ni kamar yadda rana daya na bar wa Allah da abin da Ya kaddara mini. Yana cikin abin da ya sa na kara tsayuwa ga taimakon ’ya’ya mata domin in yi iya kokarina in ga ba su shiga cikin irin halin da na shiga ba. Da zaran na ji mace na da wata matsala zan yi tsaye da shawara da abin da nake iyawa gare ta gwargwadon halina in tabbatar irin abin da na gani ba ta gan shi ba, wannan shi ne kalubalena.
Wadda nake koyi da ita a rayuwa
Ban cika koyi da mata ba; na fi koyi da maza, nakan yi kokari in yi koyi da maza a halayyar rikon bakin ciki da jure wahala
mai tsanani da boye halin da mutum ke ciki. Ina karfafa zuciyata ta zama mai karfi domin taimakon jama’a. Ina koyi da Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello. Ina son in bar abin koyi kafin in rasu, amma a bangaren rubutu na fi yin wanda suka shafi mata.
Burina ya cika
Burina ya fara cika saboda kana ganin yadda mata ke zuwa da korafi wajena ina iyakar kokarina waje magance su. Abin da yake daga mini hankali bai fi yadda bincike ya nuna mafi yawan mata a yau ba su san akwai Allah ba; sun fada cikin harkar tsafe-tsafe irin barnar da suke aikatawa da sun san Allah da kwakwalwarsu ba ta juye ba. Ina burin ganin mata sun fita daga cikin wannan fitina su koma ga karantarwar Annabi (SAW) sau da kafa, duk wani surkulle su jefar da shi bayan bayansu.
Abin da nake son a tuna ni da shi
Ina son a rika tunawa da ni a matsayin mace mai fada wa mutane su ji tsoron Allah su rike amana duk in da suka samu kansu. Ina son al’umma ta ji dadi, ba na son mutum ya ce shi ba zai shiga abu ba sai wanda zai samu kawai. Ina son a tuna ni a mace ce mai son talaka ya tsaya a matsayinsa, a mutunta dan Adam. Ina kuma son duk wanda Allah Ya hada ni da shi, in yi masa alheri in taimake shi da rayuwarsa. Ina son zaman lafiya da yafiya da taimakon juna a tsakanin al’umma da za a samu yafiya ga jama’a da an samu salama.
Tarbiyar mata a yanzu
Mata na neman ilimi, sun fi maza neman ilimi da mayar da hankali ga ilimin; amma wadansu matan ilimin ba ya amfani gare su. Yawan mata na neman ilimi ko domin sun fi yawa ne? Akwai damuwa gaskiya yadda mata ke neman ilimi amma barnarsu na kara yawa ko ba su aiki da ilimin nasu ne ko kuma suna neman ilimin ne ba su samunsa, ko kuma suna samu amma ba ya da albarka.
Shawara ga mata
Su tsaya matsayinsu na addini da Allah Ya ajiye su. Domin addini ya girmama mace. Mata su fita batun daidaito da maza a bisa gaskiya ba zai yiwu ba, ba don Allah Ya fifita maza shi ne ke nuna mu ba wata halitta ba ce, a’a Allah Ya ce maza su kula da mu. Mata na da shamaki a kokarin neman jagoranci na gaba daya, kuskure ne mace ta nemi Gwamna ko Shugaban Kasa ko Shugaban Karamar Hukuma. Amma tana iya jagoranci karkashin kulawar maza, kwamishina ko wani abu irinsa.