Dajin ’Yuga: Daga Sambisa zuwa Rugu

Sunan dajin ’Yuga  da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi ya fara amo ne sakamakon mamayarsa da mayakan Boko Haram suka yi a karshen shekarar 2013 zuwa farkon shekarar 2014, bayan da aka fara fatattakarsu daga dazukan garuruwan Shadarki da Dauduwo da Soro da Miya da Yalwan Darazo da ke iyaka da dajin Balmo […]

Dajin ’Yuga: Daga Sambisa zuwa Rugu
Dajin ’Yuga: Daga Sambisa zuwa Rugu

Sunan dajin ’Yuga  da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi ya fara amo ne sakamakon mamayarsa da mayakan Boko Haram suka yi a karshen shekarar 2013 zuwa farkon shekarar 2014, bayan da aka fara fatattakarsu daga dazukan garuruwan Shadarki da Dauduwo da Soro da Miya da Yalwan Darazo da ke iyaka da dajin Balmo kananan hukumomin Ganjuwa da Darazo da ke jihar. Rahoton da jaridar Daily Trust ta buga a karshen watan Mayun, 2014 ta ruwaito mutanen yankin da suka nemi a sakaya sunayensu saboda dalilai na tsaro suna cewa mayakan Boko Haram sun kafa sansanoni a dazukan Balmo da ke karamar Hukumar Darazo da kuma dajin ’Yuga da ke karamar Hukumar Toro wanda kuma ya yi iyaka da dajin Falgore da ke karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano zuwa kananan humumomin Ganjuwa da Ningi a Jihar Bauchi ya tokari Jihar Jigawa da kuma Tudun Wada da Kibiya da Sumaila a Jihar Kano da kuma Lere a Jihar Kaduna.
Sakamakon yadda ’yan Boko Haram din suka fara zama barazana a dajin wanda ga Fulanin da suke bin labi suka ce ya hade da dajin Sambisa a gabas kuma ya nausa zuwa kudancin kasar nan, sojoji sun fara kai farmaki a wuraren da ake kyautata zaton wuraren bayar da horo ne ko maboyar mayakan na Boko Haram a ranar Alhamis 22 ga Mayu, 2014, inda aka ce jiragen yaki na soji sun yi rowan bama-bamai ga maboyarsu.
dage zaben da gwamnatin Jonathan ta yi don kaddamar da yaki a kan Boko Haram, tabbas ya yi matukar amfani wajen fatattakar mayakan Boko Haram din daga dajin ’Yuga da aka fi sani da dajin Lame/Burra. Domin kafin hakan mayakan na Boko Haram har sun fara fitowa suna kai hari kan masu wucewa a babbar hanyar Bauchi zuwa Jos, kuma suna barazanar hana mutanen yankin yin noma. Wata majiya ma ta taba shaida min cewa, wadansu daga cikin ’yan Boko Haram din sun rika cewa wa mutanen yankin, “Kuna jin za ku yi noma bana ne? Muna shaida muku za mu kaddamar da yaki ne a bayan zaben 2015, amma babu ruwanmu da ku da gwamnati muke fada.” Wadannan kalamai sun firgita mutanen da ke zaune a yankin na dajin ’Yuga, inda ma’aikatan gwamnati da ke yankin kamar malaman makaranta da malaman jinya da jami’an tsaro suka rika kaurace wa yankin.
Sai dai ana fatattakar ’yan Boko Haram din ba a je ko’ina ba, sai kuma wadansu sababbin ’yan bindiga suka mamaye dajin. ’Yan bindigan sun fara ne da sace shanu, suka koma suna garkuwa da Fulani masu shanu suna amsa kudi, daga baya suka bazama yin garkuwa da kowa da kowa. Wani Bafullace ya shaida wa wannan marubuci cewa irin abin da masu garkuwa da mutanen suke yi har sun gwammace zama da ’yan Boko Haram, saboda su suna fada ne da gwamnati ba da talakawa ba. Ya ce amma wadannan barayin shanu da suke garkuwa da mutane suna musguna wa kowa a yankin.
’Yan bindigan sun ci gaba da yin karfi a wannan yanki inda suka rika kai hare-hare suna sace mutane a kananan hukumomin Toro da Kibiya da Ningi da Ganjuwa da Doguwa da ke kusa da dajin na ’Yuga, wanda hakan ya mayar da shi tamkar dajin Rugu.
Ayyukan tu’annati na masu garkuwa da mutanen yana kara kamari a baya-bayan nan, lamarin da ya sake jawo hankalin sojoji su sake komawa dajin.
A makon biyu da suka gabata dai sojojin sun shiga daji ta kusurwoyi da dama, Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya fadi a wata sanarwa cewa sojojin sun kai farmaki a Dutsen Mairama da yankin Dogon Ruwa da ke dajin na Lame/Burra (’Yuga) da ke yankunan Toro da Ningi, a ranar Lahadi 21 ga Agustan bana, inda ya ce: “A yayin fafatawa an kasha masu garkuwa da mutane su uku kuma aka lalata sansaninsu. Kuma sojojin sun kwato bindigogi da harsasai. Kuma ya yi alkawarin za su ci gaba da kai hari ga maboyar masu garkuwa da mutanen da ’yan fashi ko ’yan bindigan da aka sani.”
A ranar Asabar da ta gabata na leka garin Nabordo matsugunin Hakimin Jama’a dan Galadiman Bauchi wanda nan ne garin Hakimin yankin don gane wa idona yadda Fulani makiyaya suke kaurace wa yankin na dajin ’Yuga. Tabbas daruruwan Fulani suna ta ficewa daga yankin kamar yadda wani Bafullace da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida min. “Akalla Fulani sama da 300 sun fice daga dajin tare da shanunsu da suka haura dubu biyar a sanina,” inji Bafullacen. Ya kara da cewa: “Rayuwarmu da tab iyalanmu tana cikin mummunan hadari. Mutanen nan ga alama suna da daurin gindi daga wadansu jami’an tsaro. Domin babban mai sayen shanun satar sananne ne a garin ’Yuga. An sha kama shi, amma bayanan da muke samu shi ne koda an kai shi Bauchi da shi da yaransa da sunan an kama su ba su kwana a tsare, maimakon haka suna kwana ne a wuri mai kyau kuma bayan kwana daya ko biyu, sai su dawo gida.”
Bafullacen ya ce, lamarin satar mutane a yankin ya faro ne da satar shanu, daga baya ne barayin suka canja salo suka koma garkuwa da masu shanun saboda ana saurin gane barayin shanun a kasuwanni.
“Amma hakna ba yana nufin sun daina satar shanun ba ne. Suna hada dukka biyun ne. Don haka zabi na karshe gare mu shi ne mu bar yankin kafin su gama tagayyara mu,” inji shi.
Wani dan banga ma da ya nemi a sakaye sunansa ya ce: “Babban maigidan barayin nan sananne ne a garin na ’Yuga, yana da daurin gindin ’yan sanda a Toro da Bauchi. Kai karewa ma a kwanakin baya da aka sace shanun Sarkin Kafin Dilimi da aka bi ta hannunsa aka ba shi wasu kudi an dawo masa da shanun. Ko yau idan aka sace maka shanu in ka bi ta hannunsa kana iya samunsu. Wannan mutum shi ne mai masaukin barayin shanun da kuma masu garkuwa da mutanen, wadanda ake ganinsu a kai a kai a gidansa.”
A ranar Juma’ar makon jiya ne Mataimakin Kakakin Sojin Birged din Atilare da ke Bauchi, Manjo Joseph Afolashade ya bayyana cewa wani shiri da suka sanya wa suna “Operation Forest Kunama,” wanda aka faro kwana 10 da suka gabata, yana samun nasara, inda ya ce a aikin da suka yi a Ungwar Dabo da fadamar Rumbu da Dogon Ruwa sun kwato shanu 100. Kuma ya ce sun kama masu garkuwa da mutane su biyu tare da kwato Naira dubu 439 a kauyen Badikko da ke kan hanyar Gumau a karamar Hukumar Toro. Ya ce sun kama Musa Bature da Ibrahim Adamu a tsakanin Rimin Zayam da Tashar Maiturare, kuma sun ce sun gudo ne daga dajin na ’Yuga  saboda farmakin sojojin, yayin da suka kama Mohammed Idris a Takandan Giwa.
Hakika sojojin sun shiga dajin ’Yuga ta hanyar Takandan-Giwa zuwa ’Yuga, to amma dawowarsu ke da wuya barayin mutanen suka sake bayyana kamar yadda wani dan banga ya shaida min a garin Nabordo. Ya ce, “Bayanan da muka samu lokacin da sojojin suka isa inda ake zargin masu garkuwa da mutanen sun yi sansani, sai suka taso wa sojojin. An ce za su kai mutum 300, suka bude wuta, inda sojojin suka kwakkwanta a kasa. Daga baya suka aika musu da wuta daga igwa, inda suka harbe daya daga cikin barayin mutanen saura suka gudu. Amma bayan kwana uku sai muka ji an ce sun dawo sun dauki baburansu da suka gudu suka bari sun koma cikin dajin. Yanzu haka suna shigowa garin ’Yuga da Mundu da Kafin Dilimi da sauransu suna harkokinsu gaba-gadi.”
Ko yaushe za a ceto mutanen yankin da ke iyaka da dajin na ’Yuga daga ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ko barayin shanu? Wannan ita ce tambayar da jama’ar yankin suke jirar amsarta daga mahukuntan karamar Hukumar Toro da na Jihar Bauchi da kuma na Tarayya.