Dakan daka, shikan daka…..
kokarin da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya yi na kafa wani kwamitin bincike a asirce don wanke Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, Pastor Ayo Oritsejafor, tare da wani takadarin yankin Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo daga zargin wata kamuyamuya ta dalar Amurkaa har miliyan tara da dubu dari uku da aka yi niyyar sayo makamai […]
kokarin da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya yi na kafa wani kwamitin bincike a asirce don wanke Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, Pastor Ayo Oritsejafor, tare da wani takadarin yankin Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo daga zargin wata kamuyamuya ta dalar Amurkaa har miliyan tara da dubu dari uku da aka yi niyyar sayo makamai da su a boye, daga kasar Afirka ta Kudu, ya nuna Gwamnatin Jonathan ta raina hankalin jama’a. An ce wai gwamnatin tarayya ta zazzabo wasu hafsoshi daga rundunonin mayakan kasar nan guda uku, ta sanya su cikin wani kwamiti na musamman don bin bahasin zargin da aka yi wa shugaban na CAN saboda zargin amfani da jirgin samansa da aka yi wajen fita da kudin daga Najeriya zuwa kasar Afirka ta Kudu, da kuma Asari Dokubo wanda aka ce wai yana daga cikin mutane ‘yan Najeriya biyu da ke cikin jirgin. Makasudin kafa wancan kwamitin binciken kuwa wai don a wanke wadancan mutanen biyu ne, da soso da sabulu, daga dukkan zargin aikata wani lafi da ake yi masu dangane da haka.
Wata kafar yada labarai, PR Media, wacce aka ce wai tana da alaka da askarawan kasar nan, ta ce wata kungiya ta musamman da ta hada da manyan jami’an tsaro da na ma’aikatar hulda da kasashen waje ta binciki batun fita da kudin don sayo makamai, ta kuma aike da sakamakon haka ga ofishin Shugaban kasa. ‘Yan Najeriya da yawa ba su ji dadin wannan al’amari ba, domin kuwa ana zargin cewa gwamnatin tarayya na da hannu cikin wannan badakalar kamar yadda Shugaba Jonathan ya ce kudin sayen makaman na gwamnatinsa ne, kuma wani bangaren ma’aikatar tsaro ne za su yi amfani da su. Kuma ai ko ba komai bai kamata mutumin da aka nuna wa yatsan zargi ya yi uwa, ya yi makarbiya ba a cikin bincike ko shari’ar da za a yi dangane da haka ba. Ashe ke nan idan aka yi la’akari da irin dangantakar da ke tsakanin Shugaba Jonathan da wadancan mutane biyun, ana iya cewa dakan daka, shikan daka aka yi wajen fitar da sakamakon da ya wanke su.
‘Yan Najeriya dai ba su saba jin ana bin boyayyiya ko barauniyar hanya wajen bin bahasin zargin da ake yi wa wasu ba, wacce ta saba yin haka a bainal jama’a don kowa da kowa ya gamsu, a kuma kawar da zargin alfasha. Idan da fadar Shugaban kasa na son tabbatar wa talakawa cewa ba ruwanta cikin waccan badakalar ai da kyale kwamitin da ta kafa don bin bahasin zargin da ake yi wa Shugaban na CAN ya zauna a bainal jama’a, ya kuma saurari shaidu daga bakin masu sha’awar bayarwa. To amma rashin yin hakan ya sa shakku a zukatan jama’a dangane da niyyar fadar shugaban kasa game da bin bahazin zarge-zargen da aka yi wa Pastor Oritsejafor da Asari Dokubo.
To amma mene ne ma na kafa wani kwamitin, musamman don bin bahasin zarge-zargen tun da dai Shugaba Jonathan ya tabbatar wa duniya cewa wadancan kudin na gwamnatinsa ne, kuma da saninsa aka fita da su ba bisa ka’ida ba don sayo makamai? Shin Shugaba Jonathan ya manta cewa ya yi rantsuwa ne cewa zai gudanar da aikinsa na Shugaban kasa ba-sani-ba-sabo ne?. To idan haka ne da wane dalili zai aikata irin waccan tabargazar da ta kai shi zubar da mutuncinsa warwas?
Baicin haka nan me ya sa aka bayyana sakamakon bahasin waccan zargin da aka yi a asirce, amma kuma ba a fayyace sunayen ‘yan kwamitin da suka yi wancan aikin ba? Mai yiwu wa ma shara karya aka yi, ba wani bin bahasi da aka yi, ana so ne dai ayi wasa da hankulan jama’a. Idan da an yi binciken gaskiya me ya hana a gayyaci masu zargin don su tsure wadanda suka zarga, domin amsa wasu tambayoyin da suka jibanci al’amuran da ake zarginsu akai? Kuma tun da aka ce kwamitin bin bahasin ya mika rahotonsa ga Shugaban kasa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, ashe ke nan shi ne ya kafa su. To me ya sa ba a sanar da jama’a game da kafa kwamitin ba sai dai kawai aka ji sakamakon da ya fitar. Kai! Wani abu sai a Najeriya!!
Gwamnati ta ki ta fayyace wa ‘yan Najeriya yadda aka yi gwamnati, wacce ke da jiragan yaki da kuma manya-manyan jirage a fadar shugaban kasa, za ta bari babban jami’in ‘yan sandan asiri na kasar nan, watau NSA, ya yi hayar jirgi daga wani kamfani mai zaman kansa don gudanar da wata harkar da ta jibanci tsaron kasa.
Yanzu dai tunda jama’a sun muzanta sakamakon wancan bin bahasin da aka yi a asirce, sa’anan kuma ba a gamsar da su ba game da matakan da aka dauka wajen yin haka, sai a yi watsi da shi, a kuma sake yin wani ingantaccen tsarin da zai bayar da dama ga dukkan wadanda ake zargi don su wanke kawunansu ta hanyar gudanar da wani sabon bincike a bainar jama’a, ba tare da wata kunbuya-kumbuya ba. Abin da ke zukatan daukacin al’ummomin kasar nan shi ne wadancan mutanen dai da aka rigaya aka zarga da aika-aikar fita da kudi zuwa sayen makamai a wata kasa can ta daban,, kuma da sunan gwamnati, a cikin jirgin da bai kamata a bayar da hayarsa ba, har yanzu masu laifi ne, domin kuma ba su kare kansu ba game da haka a bainar jama’a. Bin bahasi ko bincike irin haka, ba a yinsa a boye, a fili ake yi don a kawar da duk wani shakku da ke zukatan jama’a. To, tun da haka Shugaba Jonathan ya yi, ana iya cewa akwai lauje cikin nadi.