Dakarun Kamaru da Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 800

Sojojin kasar Kamaru sun ce sun kashe mayakan Boko Haram kimanin 600, bayan da suka kai hari a garin Fotokol da ke kan iyaka, inda suka kashe kimanin mutanen garin 80, tar da raunata akalla wasu 120 a shekaranjiya Laraba. Bayanai sun nuna cewa kimanin mayakan kungiyar Boko Haram dubu daya ne suka far wa […]

Dakarun Kamaru da Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 800
Dakarun Kamaru da Chadi sun kashe ’yan Boko Haram 800

Sojojin kasar Kamaru sun ce sun kashe mayakan Boko Haram kimanin 600, bayan da suka kai hari a garin Fotokol da ke kan iyaka, inda suka kashe kimanin mutanen garin 80, tar da raunata akalla wasu 120 a shekaranjiya Laraba.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mayakan kungiyar Boko Haram dubu daya ne suka far wa garin, inda daga cikinsu aka kashe kimanin 600.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa sun bambance gawarwakin mutanen gari da na ’yan kungiyar Boko Haram ta hanyar kayan da ke suke sanye da su da kuma irin makamansu.
Mutanen sun ce sun bisine da yawa daga cikin gawarwakin mutanen gari, amma ba su taba na mayakan Boko Haram ba.
Rahotanni sun ce hukumomin Kamaru da na Chadi sun girke karin dakaru a Fotokol, domin dakile duk wani farmaki da mayakan Boko Haram za su nemi sake kaiwa.
kasar Chadi ma ta ce ta kashe mayakan Boko Haram fiye da 200 a wata arangama da suka yi a garin Gamboro da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Hukumomin kasar Chadi sun ce su ma an kashe musu sojoji tara, sannan aka raunata 21 a tashin hankalin da ake ci gaba da fuskanta a wasu jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sanarwar da sojin Chadi suka fitar ta ce har yanzu ana ci gaba da gumurzu domin murkushe ayyukan ’yan Boko Haram. Dakarun Chadi kusan 2,000 ne suka shigo Najeriya domin kawo karshen kashe-kashen da Boko Haram ke yi.
A farkon wannan mako ne dakarun Chadi suka soma kwato garuruwan da ’yan Boko Haram suka kwace a Najeriya.