Dakarun Kamaru sun ceto Bajamushen da ’yan Boko Haram suka sace
A makon jiya ne dakarun kasar Kamaru suka samu kwato wani Bajamushe mai suna Nitsch Eberhard Robert da aka ce kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da shi a Najeriya a watan Yunin bara. Rahotanni sun ce jami’an tsaro na Kamaru ne suka samu jubutar da shi a hannun ’yan kungiyar. Sanarwar ba ta yi […]
A makon jiya ne dakarun kasar Kamaru suka samu kwato wani Bajamushe mai suna Nitsch Eberhard Robert da aka ce kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da shi a Najeriya a watan Yunin bara.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro na Kamaru ne suka samu jubutar da shi a hannun ’yan kungiyar. Sanarwar ba ta yi bayani kan yadda aka ceto shi ba, sa’annan kuma ko a wani irin halin koshin lafiya Bajamushen yake ciki ba. Sai dai daga bisani wasu bayanai sun nuna cewa Nitsch Eberhard Robert malamin makaranta ne a wata cibiyar horarwa na garin Gombi na Jihar Adamawa da ke Najeriya. Sai dai kuma sakin ya zo ne kwana guda bayan fitowar wani faifan bidiyo, inda Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ba ma wasu kasashen Afirka kashedi wadanda suke yakarsu kamar Kamaru da Chadi da kuma Nijar wadda ta karbi bakuncin taron yaki da ta’addanci, kwanakin baya. Har ila yau, ya dauki alhakin harin da ya aukar da kisan rayukan jama’a a garin Baga a farkon watan nan, inda ya ce: “Mu muka kashe mutane a garin Baga, mun yi kuma haka ne bisa ga umarnin da Ubangiji ya ba mu a cikin littafinsa mai tsarki,” inji shi.
Kwanaki biyu bayan ya kubuta Nitsch Eberhard Robert ya gana da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya a fadarsa da ke Yaounde. Jakadan kasar Jamus ya shaida wa Mista Biya cewa Jamus za ta ci gaba da taimaka wa Kamaru yakar Boko Haram. Sai dai kuma akwai alamun cewa itama kungiyar Boko Haram ta lashi takobin tsayawa daram domin ta tunkari taron gwanon da ake yi mata. Hakan na iya tabbata ne akan rubanya kai hare-haren da take yi kusan a kullum a kuma wurare daban-daban a lokacin da ake titsiye dakarun kasar Chadi a sassan daban-daban domin su dafa wa na Kamaru baya. Har ila yau, kungiyar ta kai hari a garin Leimari mai tazarar kilometa takwas da garin Fotokol mai iyaka da Najeriya. Rahotannin sun ce a musayar harbe-harben da aka yi a tsakanin bangarorin biyu, mutane 12 sun hallaka daga bangaren Boko Haram da kuma tarin wasu da aka kama. Daga sashen dakarun kasa kuma an ruwaito cewa wani adadi kalilan ne suka jikkata. Harin garin Leimari wanda shi ne na baya-baya nan a cikin jerin hare-haren kungiyar Boko Haram yazo ne a lokacin da kasashen Hukumar Habaka Tattalin Arzikin yankin Afirka ta Tsakiya suka bayanna kansu, inda suka nuna goyon bayansu ga Kamaru tare da yin Allah-wadai game da ta’addacin da kungiyar Boko Haram take haddasawa. Wannan Hukumar da Shugaban kasar Chadi Idriss Deby yake jagoranta a wannan karo ya kunshi kasashe akalla 11.
Har ila yau, Ministan Tsaron kasar Faransa Jean Ybes Le Driant, a shekaranjiya Laraba ya jaddada kira ga kasashen yankin Afirka ta Tsakiya da su hada kai domin mayar da martani ga hare-haren kungiyar domin kaucewa rashin zaman lafiya da ka iya addabar yankin baki daya. Ministan ya ci gaba da cewa kasarsa za ta shiga wannan yakin ne domin nuna goyon bayanta da kuma taimakawa wajen hadin kai ga wani abu tabbatacce da zai taimaka wa Najeriya sake cin moriyar tsaro da kuma wasu kasashen da suka makwabtaka da ita.