Dakarun kasar Chadi sun kwato garin Gamboru
Al’amurra sun fara koma wa a garin Fotokol garin da kungiyar Boko Haram ta karbe, kwana guda bayan dakarun kasar Chadi sun samu karbo garin daga hannun ’yan kungiyar bayan wani hari na farko da suka kai musu ta kasa. An kwashe watanni dai garin yana karkashin ikon kungiyar wadda ta ja daga ta kan […]
Al’amurra sun fara koma wa a garin Fotokol garin da kungiyar Boko Haram ta karbe, kwana guda bayan dakarun kasar Chadi sun samu karbo garin daga hannun ’yan kungiyar bayan wani hari na farko da suka kai musu ta kasa.
An kwashe watanni dai garin yana karkashin ikon kungiyar wadda ta ja daga ta kan gadar El Beid wadda ita ce iyaka tsakanin garin Fotokol a Kamaru da kuma Gamboru a Najeriya.
An ruwaito cewa, kungiyar Boko Haram ta yi haka domin toshe hanyar da kayan aiki da kuma abinci suke shigewa gabannin su cinma dakarun kasar Chadi. Sai dai har zuwa wannan lokacin, babu wani bayanin da ya nuna cewa dakarun tsaron Kamaru da suke kan iyaka sun mayar da martani.
Al’amarin kuma ya sake jefa jama’a cikin wani yanayi na firgici, inda akasari daga cikinsu suka tsere zuwa daji domin neman kubuta da rayukansu. Har ila yau, a cikin kwanakin da suka gabata yakar kungiyar Boko Haram ya tsananta tun lokacin da kasar Chadi ta aika dakarunta zuwa kan iyakokinta da Nijar da kuma Najeriya. Hakan ya kai ga dakarun na Chadi da na Kamaru hada karfinsu guri guda da nufin kawar da kungiyar Boko Haram, inda ta kafa sansanoninta.
Sai dai kuma wasu rahotanni na cewa akalla gawawwakin dakarun kasar Chadi tara ne aka shiga da su garin Fotokol sakamakon karawar da suka yi da ’yan kungiyar Boko Haram a garuruwa kamarsu: Gamboru Ngala da kuma Wulgo inda sojojin suka yi wa ’yan kungiyar dirar mikiya. Hakan ya sa aka bude iyaka wato gadar da ta hada kasar Kamaru da Najeriya domin amfanin dakarun kawai.
Jami’an tsaron kasar Chadi sun ketara zuwa Najeriya domin aiwatar da yarjejeniyar da take a tsakanin kasashen biyu wadda ta ba dakarun kowace kasa shiga cikin makwabciyarta da nufin bin sahun kungiyar. Wannan shi ne abin da tun farko gwamnatin Kamaru ta ki amincewa da shi ke nan. Amma kuma a kokarin cinma burin da suke so su yi, dakarun hadin gwiwa sun nemi agajin wasu matasa da suke iya tantance sako-sakon Gamboru domin su shiga su zakulosu a duk inda suka.