Dakarun Nijar sun ceci sojojin Najeriya daga harin ’yan bindiga
An ceci sojojin bayan ’yan bindiga sun kashe wasu akalla 12 a Jihar Sakkwato.
Dakarun sojin Jamhuriyar Nijar sun ceci wasu sojojin Najeriya tara da suka janye bayan ’yan bindiga sun kai musu hari a Jihar Sakkwato.
Dakarun Nijar din sun ceto sojojin na Najeriya ne a kauyen Basira da ke lardin Gidan Roumdji na Jamhuriyar Nijar a ranar Juma’a.
- Kasurgumin mai garkuwa da mutane na neman a yafe masa
- Abin Da Shugaba Buhari Ya Fada Wa Majalisar Dinkin Duniya
Idan ba a manta ba mun kawo rahoton yadda ’yan bindiga suka kai wa jami’an tsaron hadin gwiwa hari a sansanin soji mai suna “Burkusuma” da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, inda suka kashe sojoji da sauran jami’an tsaro da dama a ranar Juma’a.
Maharan sun kuma kai hari a kauyen Gatawa da sauran yankunan.
Ba a samu labarin lamarin na sai ranar Lahadi, sakamakon toshe layin sadarwa a jihohin Zamfara da Sakkwato da Katsina.
Wani dan Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, Aminu AlMustapha Gobir, ya tabbatar wa Aminiya cewa jami’an tsaro 12 ne ’yan bindigar suka kashe a harin.
Amma Kwamishinan Tsaron Jihar Sakkwato, Garba Moyi, ya ce babu tabbaci game da yawan wadanda suka rasu a harin.
Aminiya ta gano cewa ’yan bindiga daga gungun da Halili Sububu da na Kachalla Turji daga Jihar Zamfara ne suke kai wa al’ummomin Jihar Sakkwato hare-hare a baya-bayan nan.
“’Yan bindida da yawa ne suka kai harin, inda suka yi wa sansanin sojin kawanya suna ruwan wuta,” inji tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir (Danchadi).
Ana fargabar soja tara, ’yan sandan kwantar da tarzoma uku da jami’an hukumar tsaro ta sibil difensu sun ne suka kwanta dama a harin na Sabon Birni, wasu da dama kuma ba a san inda suke ba.