Dakatar da albashi: NASU da SSANU sun tsunduma yajin aiki
Ƙungiyoyin sun ce rashin biyan su albashin ya jefa su cikin tsaka mai wuya.
Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i, sun tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyan su albashi wata huɗu.
Gamayyar ƙungiyoyin (JAC), waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASU) da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i na Najeriya (SSANU).
- Muna aiki tuƙuru don gyara wutar Arewa — TCN
- El Classico: Barcelona ta yi wa Real Madrid zazzaga har gida
A cikin wata sanarwa da ta aike wa dukkanin shugabannin ƙungiyar da ke jami’o’i da su fara yajin aikin a ranar Lahadi.
Sanarwar, wadda Sakataren NASU, Mista Peters Adeyemi da Shugaban SSANU, Mista Mohammed Ibrahim, suka sanya wa hannu, a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce: “Mun yanke wannan hukunci ne sakamakon dakatar da albashinmu ja wata huɗu.”
Duk da cewar Shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan kashi 50 na albashin da aka dakatar, amma JAC ta ce babu wanda ya samu ko sisi daka cikinsu.
JAC, ta bayyana cewa ta gargaɗi gwamnati a lokuta daban-daban, amma ba a yi komai kan buƙatarsu ba.
Saboda haka, JAC ta yanke shawarar cewa za a fara yajin aikin ne misalin ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024.
Ƙungiyar ta ce sai gwamnati ta waiwaye sannan za su janye yajin aikin da za su fara a daren yau.