Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan
Yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangarorin gwamnati suka ɗauka.

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara da aka yi kwanan nan zubar da ƙimar ƙasar ne a idon duniya.
Tsohon shugaban ya ce ba daidai ba ne dakatar da Gwamnan Ribas da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da ’yan majalisar dokokin jihar, wanda Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon jiya.
- An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar
- An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
Channels TV ta ruwaito Jonathan yana bayyana haka yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja.
Jonathan wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni da aka yi.
“Wannan matakin da aka ɗauka zai ɓata sunan Nijeriya ne a idon duniya,” in ji shi.
Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.
Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da ke faruwa a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Nijeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.
A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a Jihar Ribas, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.