Dakatar da jigilar jirgin kasan Abuja-Kaduna ta jawo asarar N3bn

Ana asarar Naira miliyan 21.6 a kullum tun bayan harin ’yan ta’adda.

Dakatar da jigilar jirgin kasan Abuja-Kaduna ta jawo asarar N3bn

Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kudaden shiga sama da Naira biliyan uku tun bayan da ta dakatar da jigilar jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Kullum ana asarar Naira miliyan 21.6 na tikitin jirgin kasan, a tsawon kwana 140 tun bayan harin ’yan ta’adda a kan jirgin kasan a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Rufe harkokin jirgin kasan ya haddasa rufe harkokin kasuwanci da sauran harkokin neman abinci da mutane ke yi a wurin.

An dakatar da jigilar jirgin kasan ne bayan harin bom din da ’yan ta’adda suka kai wa jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna dauke da mutum 970.

Maharan sun kashe kimanin 10 daga cikin fasinjojin, suka yi garkuwa da wasu 60, baya ga wadanda suka jikkata a sakamakon harin.

A sanadiyyar haka ne Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da harkokin jirgin sai abin da hali ya yi.

’Yan ta’addan sun sako wasu daga cikin fasinjojin bayan an biya kudaden fansa, amma har yanzu akwai wasu a hannunsu.

A halin da ake ciki, NRC ta ce ba za ta ci gaba da gudanar da harkokin jirgin kasan Kaduna-Abuja ba har sai an sako duk fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Yadda aka yi asarar N3.024bn na tikiti

Binciken Aminiya ya gano kawo yanzu, a kwana 140 da aka dakatar da harkokin jirgin, hukumar NRC ta yi asarar Naira biliyan 3.024 na tikitin jirgin da ya kamata a ce ta sayar a tsawon lokacin.

Jirgin da ke zirga-zirga tskanin tashar Idu da ke Abuja zuwa tashar Rigasa a Kaduna, na daukar fasinja 900 zuwa 1,000 a duk sawu.

Kullum jirgin kan yi sawu takwas kuma farashin matsakaicin tikiti N2,800 zuwa N3,000 ne, na kujerar alfarma kuma N6,000. 

Kididdigar da Aminiya ta yi ya nuna a duk sawu na jirgin mai daukar mutum 900 zuwa 1,000, gwamnati za ta samu Naira miliyan 2.7 idan aka sanya farashin tikiti a N3,000.

Sawu takwas, rana guda ke nan, za a samu Naira miliyan 21.6, a mako guda kuma Naira miliyan 151.1 za a samu daga sayar da tikiti.

A kwana 140 da rufe harkokin harkokin jirgin kasan daga ranar 28 ga wata Maris zuwa 15 ga Agusta, asarar da Gwamnatin Tarayya ta yi ya kama Naira biliyan 3.02 na tikiti kawai.

Asarar ta wuce iya kudin tikiti –Kwararru

Wasu kwararru da muka tattauna da su sun bayyana cewa asarar da dakatar da sufurin jirgin kasan ke haifarwa ba na kudin sayar da tikiti ba ne kawai.

Bincikenmu ya gano harkokin kasuwancin ’yan tireda da sauransu da suka dogara da zirga-zirgan jirgin a tashar jirgi da ke Idu da Kubwa a Abuja da kuma Rigasa a Kaduna sun tsaya.

Masu irin wadanann harkoki da ba su sauya wuri ba bayan dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan, sun sallami ma’aikatansu.

Wata mai gidan abinci a tashar Idu, Halima Abubakar ta ce, “Tun washegarin harin jirgin kasan na rufe shagona.

“Komai ya tsaya cik… Na sallami ma’aikatana saboda ban samu wani wuri da zan koma ba.”

Su ma direbobin haya, ’yan tasi da dangoginsu da ke samun kudade ta hanyar jigilar fasinjojin jirgin kasan, harkokinsu sun tsaya.

A kan haka ne wani direban tasi a tashar Idu, Ambrose Alex, ya yi kira ga gwamanti ta dauki matakin da ya dace

“Duk an watsa harkokinu a sakamkon rufe tashoshin jirgin kasan; Ni bashi na ciyo na sayo motar da nake haya a tashar jirgin kasan.

“Abubuwa sun yi wuya yanzu, wadansunmu sun koma aiki a cikin gari maimakon daukar shata, wadda aka fi samu da ita.”

Haka kuma Aminiya ta gano NRC na kara yin asara a bangaren kudin haya.

Karshenta sai dai ta mayar wa masu haya a tashoshin kudadensu, ko ta kara musu lokaci daidai da yawan watannin da aka rufe harkokin.

Wani karin asarar kuma shi ne ga kamfanin tikitin jirgin kasan, SevureID Solutions, wanda aka bai wa kwangilar Naira miliyan 900 ya yi aiki na tsawon shekara 10.

Saboda rashin samun kudaden shiga daga jirgin kasan, akwai yiwuwar kamfanin ya sallami ma’aikatansa ko ya nemi kwaskwarima a kwangilar da aka ba shi.

Wani kwararre a fannin sufuri daga Kwalejin Kasuwanci ta Legas, Dokta Frank Ojiadi, ya bayyana cewa baya ga gwamnati, har ’yan Najeriya sun tafka asara mai yawa a sakamakon dakatar da harkokin jirgin kasan.

Ya bayyana cewa “Wannan zaman jiran da ake ta yi a bangaren sufurin jiragen kasa ya faru ne a sanadiyyar abubuwa da dama.”

Ya ce hakan ba za ta yiwu ba a bangaren sufurin jiragen sama saboda muhimmancinsa ga tattalin arzikin kasa da kuma karfin inshorar bangaren.

A cewarsa, babu yadda za a yi a rufe sufurin jiragen sama kacokan saboda harin ta’addanci.

Don haka masanin ya ce ya kamata NRC ta tabbatar an yi wa jiragen kasa inshora.

Ya bayyana cewa dakatar da jigilar jirgin na yin illa ga tattalin arziki da kuma yanayin rayuwa a Najeriya.

A bangaren tattalin arziki, a cewarsa, Gwamnatin Tarayya za ta yi babbar asara saboda NRC ba ta samun kudaden shiga.

Sannan kanyan aiki za su samu matsala ko ma su lalace saboda dadewa ba sa aiki.

“Kayan aiki da na’urori da ba a aiki da su za su iya yin rauni.

“Sannan za a takura wa tituna saboda yawan matafiya; A baya jirgin kasan ya rage yawan motocin da ke bin tituna.”

Ya kara da cewa mutane kuma za su fuskanci barazanar harin ’yan ta’adda a kan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.

Sauran bangaren da abin zai shafa shi ne harkokin kasuwancin da jirgin kasan ya kawo a yankunan da tashoshinsa suke.

Ya ba da shawara cewa idan aka ci gaba da zirga-zirgar jirgin, to ya kamata a daina tafiya da dare saboda hadarin ya fi yawa a cikin duhu.

‘A kawar da matattarar ’yan ta’adda don ci gaba da harkokin’ 

Wani kwararre a fannin tsaro, Ibrahim Sani, ya ce kasada ce a ci gaba da zirga-zirgar jirgin kasan  Kaduna zuwa Abuja ko da ’yan ta’adda sun sako fasinjojin da ke hannunsu.

“Na lura wasu mutane suna kallon matsalar ce ta fuska guda, amma wannan babbar matsala ce da ke bukatar gwamanti ta yi abin da ya dace,” in ji Sani, wandan Kanar din soja ne mai ritaya.

“Akwai ’yan ta’adda a yankin da jirgin kasan Abuja-Kaduna ke bi; idan har ana so a ci gaba da harkokin kuma ya yi wani amfani, to dole gwamnati ta bi ’yan ta’addan har maboyarsu ta gama da su.

“Dole a samar da aminci a kauyukan ba tare da tsoro ba, kuma idan gwamnati ta ga dama za ta iya. 

“’Yan ta’adda ba su suka fi kowa iya tashin hankali ba kuma ba aljanu ba ne daga wata duniya suke zuwa su addabi mutane — Ai an san maboyarsu,” in ji shi.

Yadda tsaikon zai shafi biyan bashi

Kwararru na ganin ba a gudanar da sufurin jirgin kasan ta yadda zai taimaka wajen biyan bashin da aka ciyo domin yin titin jirgin.

Wani masanin tattalin arziki, Tope Fasua, ya ce, “Har yanzu bata-garin ’yan Najeriya na amfani da jirgin kasan suna tatsar kasar. 

“Babu alamar da ke nuna gwamnati na so ta gudanar da jirgin kasan ta yadda za ta yi amfani da kudaden da take samu wajen biyan bashin aikin da ta ciyo.”

Masanin ya bayyana cewa, kudaden da ake samu daga sayar da tikitin jirgin ba su da iyaka idan aka kwatanta da rancen da aka karbo domin yin aikin.

Ya kara da cewa a sauran kasashen duniya gwamnatoci na gudanar da sufurin jiragen kasa ne ta hanyar bayar da tallafi domin mutanen kasa su sami saukin zirga-zirga.

Railway Technology, ya bayyana cewa an kashe Dala biliyan 874 a aikin titin jirgin kasan Abuja  zuwa  Kaduna da kamfanin CCECC na kasar China ya gina.

Bankin China EXIM ya bayar da rancen Dala milliyan 500 domin aiwatar da aikin ga gwamnatin Najeriya, wadda ita kuma ta biya cikon kudaden.

Ana sa ran kammala biyan bashin ne ga bankin China EXIM a watan Satumban shekarar 2030, da kudin ruwa kashi 2.5 ckin 100.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Philip S. Clement, Sunday M. Ogwu & Chris Agabi