Dakatar da ma’aikatan bogi ta hanyar fasahar sadarwa na samar da Naira biliyan 24.3 duk wata – Buhari

Shugaban Muhammadu Buhari, ya ce Gwamnatin Tarayya tana adana Naira biliyan 24.3 a duk wata sakamakon sabon tsarin da gwamnati take aiwatarwa a kan hada-hadar kudade. An bayyana hakan ne lokacin taron gudanar da harkokin Najeriya ta na’ura wanda Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA) ta shirya. Shugaba Buhari ya ce tsarin […]

Dakatar da ma’aikatan bogi ta hanyar fasahar sadarwa na samar da Naira biliyan 24.3 duk wata – Buhari

Shugaban Muhammadu Buhari, ya ce

Shugaban Muhammadu Buhari, ya ce Gwamnatin Tarayya tana adana Naira biliyan 24.3 a duk wata sakamakon sabon tsarin da gwamnati take aiwatarwa a kan hada-hadar kudade.

An bayyana hakan ne lokacin taron gudanar da harkokin Najeriya ta na’ura wanda Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA) ta shirya. Shugaba Buhari ya ce tsarin hadahadar  kudade ta asusun bai daya TSA ya taimaka wajen samar da wasu karin kudade wanda a yanzu haka an samu naira biliyan 1.6.

Shugaban ya ce, shirin da aka kaddamar na tsarin TSA ya taimaka wajen biyan kudade da samun bayanan wasu jama’a da ke harkar kudade da lambar BBN na rijistar masu asusun ajiya a bankunan kasar wanda hakan ya taimakawa gwamnati wajen samarwa kasar kudaden ajiya a asusun gwamnati.

Bugu da kari hadakar asusun ajiya a bankuna Najeriya ya rage ma’aikatan bogi tare da samar da kudaden ajiya da ya kai naira biliyan 24.7 yayin da tsarin TSA yasa aka samu rarar kudaden ajiya har da kudin da aka samu kwanan nan na naira biliyan 1.6, in ji shi.

Shugaban kasar ya ce, wannan tsarin ya taimaka wajen yakar cin hanci da rashawa da gwamnati take yi don tabbatar da adalci da gaskiya a harkokin kasuwancin gwamnati.

Hukumar NITDA dai na fuskantar ayyukan da ya shafi rijistar ‘yan kwangila fasahar sadarwa da kuma masu kamfanonin sadarwa don tabbatar da sahihancin ayyukan kamfanonin fasahar sadarwa, wannan zai tabbatar ingancin ayyukan da suka sa gaba, da bunkasa kamfanonin ciki gida don su ma  su shiga sawun kamfanonin da suke gasa a fannin.

Duk da haka shugaban kasar ya ce, akwai hukuncin da aka tanadar ga wadanda suka karya dokar gwamnati kamar yadda aka sanar cewa, kowa ne kamfanin fasahar sadarwa ba zai fara aiki ba har sai hukumar NITDA ta tantance su.

Ya ce, hakan ya biyo bayan umarnin gwamnati na cewa, duk kamfanonin fasahar sadarwa sai sun amince da sharuddan da gwamnati ta gindaya akan tsare-tsaren wanda hakan zai taimaka wajen tattala kudin ajiya da kuma ingancin ayyukan da ake gudanar wa da kaucewa kalubalen da wasu suke fuskanta.

“Ana tsammanin hukumar NITDA ta yi aiki da hukumomin gwamnati don tabbatar da kamfanonin sun a bin tsarin da aka gindaya masu. Kamfanonin fasahar sadarwa da aka samu da laifi za a kai karar su ga gwamnati”.

“A shirye gwamnati take wajen yaki da rashawa. Muna kokarin ganin mun dakile rashawa a harkokin kasuwancin gwamnati da kuma cikin al’umma baki daya” in ji shugaban.

Shugaban kasar ya ce, shirin ‘Social Inbestment Programme (SIP)’, wanda yana daya daga cikin shirin da gwamnati ta yarda da shi a bangaren manhajar fasahar sadarwa.

Wasu bangare na shirin sun hada da: ‘N-Power, Gobernment Enterprise da Empowerment Programme (GEEP), Home Grown School Feeding Programme (HGSFP) da Conditional Cash Transfer (CCT)’ wanda duk kansu sun raja’a a fannin fasahar sadarwa. Akalla ‘yan Najeriya miliyan tara ne suka mafaana daga shirin.

Ya kuma ce, hukumar NITDA tana hada gwiwa da hukumar ‘National Social Inbestment Office (NSIO)’, wanda take lura shirin gwamnatin tarayya a  kowan ne shiyyoyi shida  a kuma cibiya daya a Legas da Abuja.

Dalilin kaddamar da wadannan shirin shi ne bunkasa harkokin fasahar zamani ta fannin koyon sana’o’in dogaro da kai, duk wadannan da nufin inganta tattalin arziki a fannin fasaha.

Shugaban ya yi murnar hada taron da aka yi ta hanyar bullo da sababbin fasahohi wanda za a iya amfana da su kuma zasu iya taimakawa gwamnati wajen samar da muhallin da zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Buhari ya sanar cewa, bangaren fasahar sadarwa ICT na samar da kashi 11.81 cikin 100 na adadin kudaden  da kasa take samku a rubu’in shekara.

Ministan sadarwa Barista Adebayo Shittu sakamakon da ake samu a bangaren fasahar sadarwa na ci gaba da koma wa baya amma ta hanyar gudunmawar da jama’a suke bayarwa da amfani da fasaha na dada bunkasa tattalin arzikin kasar.

Darakta Janar na Hukumar NITDA Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce Hukumar tana kokarin tabbatar ilimin fasahar zamani da ake samu zai iya inganta tattalin arzikin kasa.

A yayin jawabin tsohon shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya ce, cin hanci da rasahawa na daga cikin abin da ya hana kasar ci gaba amma a yanzu ta yin amfani fasahar zamani komai na bunkasa.