Dakatar da Rahama Sadau ba zai canza komai ba a Kannywood —Farida Jalal
Yawancin masu zagin Rahama Sadau a Kannywood na da kashi a gindi, inji Farida Jalal.
Jaruma a masana’antar finm na Kannywood, Farida Jalal ta ce dakatarwar da Kungiyar Masu Shirya Fina-finai (MOPPAN) ta yi wa Rahama Sadau ba zai shafi kimar jaruman masana’antar ba.
Farida Jalal ta ce wajibi ne shugabannin Kannywood su bullo da sahihan hanyoyin hukunta masu laifi ba dakatarwa ko korar su ba.
Don ma’aurata: Bayani kan soyayya…
Gayyatar Rahama Sadau muka yi ‘Yan sanda
“Ba yanzu Rahama ta fara ba kuma babu abin da ya sauya, saboda haka ina ganin babu sauyin da dakatarwa ko kora zai kawo”, inji ta.
Ta bayyana haka ne a bayaninta game da kurar da ta tashi bayan wani ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW) sakamakon hotunan da Rahama ta wallafa a Twitter.
Farida ta ce duk da cewa Rahama Sadau ce ta jawo wa kanta abin da ya same ta, amma yawancin masu harka a masana’antar masu laifi ne.
“Abin takaici ne yadda yawancinmu a masana’antar ke zagi da la’antar ta alhalin kowannenmu na da kashi a gindi.
“Ita ta jawo duk abin da ya faru saboda mugun abin da ta yi, amma tunda ta yi nadama ta tuba, ya kamata a yafe mata”, inji ta.
A cewarta, duniya ba za su daina kallon jarumar a matsayin ’yar Kannywood ba da kuma danganta duk abin da ta yi da masana’antar.
Farida Jalal ta kirayi ’yan Kannywood da su mayar da hankalinsu kan yadda za su bunkasa masana’antar ba tozarta junansu ba.
A hirar da jaridar intanet ta Kano Focus ta yi da jarumar, ta shawarci takwarorinta su rika bin koyarwar Musulunci a harkokinsu a koyaushe.