Dakatar da Rahama Sadau ta haifar da sabuwar takaddama
Kimanin watanni biyu ke nan da kwamitin ladabtarwa na Masana’antar Fina-finan Hausa ya dauki matakin dakatar da fitacciyar ’yar fim, Rahama Sadau daga sana’ar fim na tsawon watanni shida a kan batun da ta yi cewa darakta kuma jarumi Adam A. Zango ya cire ta a wani fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta’ sakamakon kin […]
Kimanin watanni biyu ke nan da kwamitin ladabtarwa na Masana’antar Fina-finan Hausa ya dauki matakin dakatar da fitacciyar ’yar fim, Rahama Sadau daga sana’ar fim na tsawon watanni shida a kan batun da ta yi cewa darakta kuma jarumi Adam A. Zango ya cire ta a wani fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta’ sakamakon kin amincewa da ta yi game da nemanta da ya yi da lalata; lamarin da ya jawo kwamitin ladabtarwar ya gudanar da binike a kan zargin nata tare da gano gaskiyar lamari cewa ’yar wasan yarfe da kage ne kawai ta yi ga jarumin.
Sai dai daukar wannan hukunci da kwamitin ya yi ya bar baya da kura, inda aka samu rarrabuwar ra’ayi a tsakanin shugabannin kungiyoyin ’yan fim din. Yayin da wasu ke ganin hukuncin ya yi daidai, wasu kuma a gefe guda suna ganin lamarin a matsayin rashin adalci ga jarumar.
Rabuwar ta bulla ne a daidai lokacin da wasu daraktocin fim din Hausan suka yi kunnen uwar shegu da hukuncin dakatarwar da aka yi wa Rahma, ta hanyar ci gaba da sanya ta a fina-finansu na baya.
Wata majiya mai tushe daga masana’antar ta bayyana cewa Darakta kuma uban gidan jarumar, wato Ali Nuhu ya rubuta takardar neman izini ga kwamitin ladabtarwar da ya yarje masa ya yi amfani da jarumar a wani fim da ya fara dauka da jarumar wanda kuma yana ganin idan har aka ce sai wata shida za a ci gaba da daukar fim din zai jawo asara ga masu fim din. An ce Ali Nuhu bai jira amsa daga kwamitin ba ya ci gaba da daukar fim din nasa da ita. Hakan ya bude kofa ga sauran daraktoci, su ma suka ci gaba da sanya ta a fina-finansu.
Ana cikin haka sai Hulumar Tace Fina-finai Da dab’i ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar jaddada wancan hukunci na dakatar da jarumar, inda ta ce daga yanzu ba za ta kara tace fina-finan da ke dauke da ita a ciki ba har sai wa’adin watanni hudu ya cika nan gaba. Hukumar ta dauki wannan mataki ne a wani taron da ta gudanar da masu ruwa da tsaki a harkar tare da wakilan jami’an tsaro na jihar a ranar 20 ga watan jiya.
Shugaban hukumar, Malam Ahmed dahiru Beli ya ce ya zama dole ga hukumar a matsayinta na uwa ga maana’antar fim ta shiga cikin lamarin, don ta kawo gyara a cikin harkar gaba daya. “Yau ka ji an ce wancan ’yar fim da wancan sun yi fada a wani wuri, sai ka ji an ce ga wasu ’yan fim sun aikata abin Allah-wadai a wani wurin daban. To, a matsayinmu na hukumar da ke sa ido ya zama dole mu yi duk mai yiyuwa don kare martabar wannan masana’anta” Inji shi.
Sai dai Abdullahi S. Abdullahi wanda aka fi sani da Baba karami, wanda kuma shi ne Shugabam kungiyar masu sana’ar fim ta Arewa Film Makers ta kasa, ya bayyana cewa kungiyarsu ba ta san da wannan dakatarwa ba. “An dakatar da ’yarmu ba tare da saninmu ba. Abin da muke cewa shi ne, kamata ya yi a shugabance mu da yawunmu, ba wai a rika yi mana mulkin kama-karya ba. Don haka a wajenmu jaruma Rahama ba dakatacciya ba ce kuma za mu ci gaba da sanya ta a fina-finanmu.” Inji shi.
Har ila yau, Baba karami ya musanta niyyarsu ta tura wakili a lokacin zartar da wancan hukunci a kan jarumar. “A matsayina na shugaban wannan kungiya, ban tura kowa a matsayin walikinmu ba a yayin zaman wancan kwamiti amma kwatsam sai na ji ana batun cewa wai da yardarmu aka dakatar da jaruma Rahama” Inji shi.
Isma’ila Na’abba Afakallah, shi ne Shugaban kungiyar Arewa Film Makers reshen Jihar Kano, ya bayyana wa Aminiya cewa kafin a dakatar da Rahama Sadau sai da kwamitin ladabtarwa karkashin jagoranci Kamilu Muhammad ya zauna da wakilan kungiyoyin masu gudanar da sana’ar fim da suka hada da na MOPPPAN da Arewa da ta Daraktoci da ta ’yan wasa da sauransu, inda suka hadu suka dauki wannan mataki a kan jarumar.
Afakallah ya kara da cewa: “Wakilan wadannan kungiyoyi su ne membobin wancan kwamiti na ladabtarwa, don haka batun wani ya fito ya nuna cewa ba shi da masaniya game da hukuncin da aka zartar a kan jaruma Rahama Sadau ba shi da tushe ballantana makama.” Inji shi.
A cewarsa, Jaruma Rahama ba ita ce farkon wacce kwamitin ya fara ldabtarwa saboda samunta da laifi ba, domin ko a baya kwamitin ya dakatar da Nafisa Abdullahi da Fati Ladan da Maryam Malika da wasu ’yan fim da dama. “Ba na mantawa wannan kwamiti ya taba dakatar da Nafisa Abdullahi da wasu ’yan fim din. Haka kuma wanann kwamiti ya taba kiran Adam Zango ya yi masa gargadi game da wani laifi. Idan an fahimta cewa wannan kwamiti yakan ladabtar da ’yan wasa daidai da giraman laifin da mutum ya aikaata. To me ya sa hukuncin da aka dauka a kan Rahama zai zama daban da na saura? Ya kamata a fahimaci cewa ba a daukar hukunci a kan ’yan fim don zalunci. Ya zama wajibi mu tallafa wa wannan sana’ar tamu don ta samu dorewa cikin mutunci” Inji shi.
A nata banagaren, jaruma Rahama Sadau ta bayyana wa manema labarai cewa ba a bi hanyar da ta dace wajen sanar da ita game da dakatarwar da aka yi mata ba. “Ina kan hanyata ta komawa Kaduna daga Kano na ji labarin dakatarwar. Na je Kano kamar sau uku a daidai wannan lokacin amam babu wani sako a hukumance da ya same ni game da waccan laifi da ake zargina da shi” Inji ta.
Sai dai kuma ana wata sai ga wata, daidai lokacin da ake wannan takaddama sai Hukumar Tace Fina-finai ta yi karar Abdullahi S. Abdullahi Baba karami gaban ’yan sanda bisa ikirarin da ya yi a wata kafar watsa labarai, cewa babu wata hukuma da ta isa ta dakatar da jaruma Rahma; haka kuma babu wanda ya isa ya hana shi yin fim da ita.
Alhaji dahiru Ahmad Beli ya tababtar wa Aminiya cewa hukumarsu na nan kan bakanta don ganin ’yan sanda sun kama darakta kuma shugaban kungiyar AFMAN na kasa, Babab karami sai dai idan ya janye batun da ya yin a izgilanci da raini ga hukumar.